Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista

Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista

- Ministan lafiya a Najeriya bayyana bukatar makudan kudade don yaki da zazzabin cizon sauro

- Ministan ya yarda kasar ba ta isassun kudade duba da yadda annobar Korona ta lalata tattalin arziki

- Ya kirayi kungiyoyi da su tallafawa gwamnati wajen yaki da zazzabin na cizon sauro a kasar

Najeriya na bukatar sama da naira tiriliyan guda domin yaki da zazzabin cizon sauro a kasar, in ji Dokta Osagie Ehanire, gidan Talabijin na Channels ta ruwaito.

Ya bayyana cewa daga cikin jimillar kudin, kasar na bukatar sama da naira biliyan 350 don yaki da cutar a shekarar 2021 kadai.

Ehanire, Ministan Lafiya, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Shehu Sani: Kashe-Kashen da Ake a Zamfara Yanzu Ya Fi Na Afghanistan

Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista
Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista Hoto: bbc.com
Asali: UGC

“Aiwatar da sabon tsarin zai ci naira tiriliyan 1.89; ana bukatar kimanin Naira biliyan 352 don aiwatar da shirin a shekarar 2021,” ya shaida wa manema labarai haka ne gabanin ranar zazzabin cizon sauro ta Duniya da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi.

Ya yarda cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da isassun kudin da ake bukata don yaki da cutar a bana.

Ehanire ya danganta hakan ne ga yanayin tattalin arzikin da ake fama da shi a sanadiyyar annobar Korona, kamar dai yadda yake a wasu kasashe.

Don haka, ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyi daban-daban, da masu kishin kasa da su ba gwamnati goyon baya don magance zazzabin cizon sauro.

KU KARANTA: Akume ya bayyana dalilan da suka sa aka gagara dakile matsalar 'yan bindiga

A wani labarin, Karin farashin abinci a Najeriya na zama abinda ba za a iya jurewa ba, ba iya ga masu saye ba har ma ga masu sayar da kayayyakin abinci.

Wata mata ‘yar kasuwa da ta zanta da Legit.ng kwanan nan ta bayyana cewa yawan mutanen da ke rokon abinci a wannan zamanin sun fi wadanda suke da halin da za su ci da kansu.

Matar 'yar kasuwa da ba ta bayyana sunan ta ba ta bayyana cewa yana da matukar wahala da tsada a yanzu a ciyar da karamin iyalin da kudin shigansu na wata-wata bai wuce mafi karancin albashin N30,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel