Sojojin Najeriya na yiwa yayanmu dauki daya-daya, Ohanaeze Ndigbo ta koka

Sojojin Najeriya na yiwa yayanmu dauki daya-daya, Ohanaeze Ndigbo ta koka

- Ana tuhumar hukumar Sojojin Najeriya da kashe matasan Igbo a boye a yankin kudu maso gabas

- Kungiyar kare hakkin yan kabilar Igbo, Ohanaeze ce tayi wannan tuhuma

- Kungiyar ta yi kira ga shugaban Sojin Najeriya ta sa baki a daina wannan kame-kame da kashe-kashe

Kungiyar kare hakkin yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu ta yi zargin cewa Sojojin Najeriya na yiwa matasan Igbo dauki daya-daya suna kashe su.

Kungiyar ta ce Sojoji na damke matasa a titi da sunan cewa mambobin kungiyar rajin kafa kasar Biyafara, IPOB, ne da kungiyar tsaron gabas ESN, kuma suna kashesu ba tare da wani hujja ba.

Wannan zargin na kunshe cikin jawabin da kakakin kungiyar, Cif Alex Ogbonnia, ya saki.

Wani sashen jawbain da Punch ta wallafa yace: "Muna kan bakanmu cewa zalunci ne a kama wani matashin Igbo da sunan cewa dan kungiyar ta'adda ne sai an gabatar da isasshe hujjar ya aikata laifi ne an gansa da makami."

DUBA NAN: Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Sojojin Najeriya na yiwa yayanmu dauki daya-daya, Ohanaeze Ndigbo ta koka
Sojojin Najeriya na yiwa yayanmu dauki daya-daya, Ohanaeze Ndigbo ta koka
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

A bangare guda, an sake kai hari kan yan Arewa mazauna jihar Imo inda aka hallaka akalla mutum bakwai,Jaridar Aminiya ta ruwaito.

A cewar rahoton, wannan sabon harin ya auku ne makon da ya gabata inda aka kashe mutum hudu a Orlu kuma mutum uku a garin Amaka.

Wani mazaunin Owerri, Dr. Lawan Yusuf, ya bayyana cewa yan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ne suka kai harin.

"Ko jiya yan IPOB sun kaiwa wasu yan Arewa mahauta hari kuma sun kashe mutum uku. Mun ji jana'izarsu," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel