An hallaka yan kasuwan Arewa a sabon harin da aka kai jihar Imo

An hallaka yan kasuwan Arewa a sabon harin da aka kai jihar Imo

- Yan Arewa sun fara kaura daga jihar Imo sakamakon harin da ake kai musu

- An kashe yan Arewa akalla 11 cikin makonni biyu da suka gabata yanzu

- Jihar Imo na fuskantar hare-hare kan yan sanda, fursunoni da yan kasuwa

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an sake kai hari kan yan Arewa mazauna jihar Imo inda aka hallaka akalla mutum bakwai.

A cewar rahoton, wannan sabon harin ya auku ne makon da ya gabata inda aka kashe mutum hudu a Orlu kuma mutum uku a garin Amaka.

Wani mazaunin Owerri, Dr. Lawan Yusuf, ya bayyana cewa yan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ne suka kai harin.

"Ko jiya yan IPOB sun kaiwa wasu yan Arewa mahauta hari kuma sun kashe mutum uku. Mun ji jana'izarsu," yace.

"Duk lokacin da suka hadu da yan Arewa a wurare kasuwancinsu, su kan tambayesu shine an basu izinin zama a kasar Biyafara, idan suka ce a'a, sai su lallasa mutum da makamansu; an kashe mutanenmu da dama ta haka."

Yusuf ya ce an tura jami'an tsaro wuraren da yan Arewa suka fi yawa ne "amma babu jami'an tsaro a wasu wuraren kuma cikin tsoro muke rayuwa."

Cikin makonni biyu da suka gabata yanzu, an hallaka akalla yan Arewa 11 a jihar Imo.

KU KARANTA: Garkuwa da dalibai: Gwamnatin Katsina ta tura Karnuka gadin makarantun jihar

An hallaka yan kasuwan Arewa a sabon harin da aka kai jihar Imo
An hallaka yan kasuwan Arewa a sabon harin da aka kai jihar Imo
Asali: UGC

KU KARANTA: Mutum 40 kacal suka halarta bana sabanin 300 a bara: Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari

Mun kawo muku rahoton cewa wasu mutanen da su ka fito daga Arewa sun fara kaura daga Imo, da-dama daga cikinsu sun koma gida.

Wani ‘dan kasuwa a Imo, Iliyasu Sulaiman, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an harbe ‘danuwansa na jini, sannan an kashe wasu mutanen Arewa uku a garin Orlu.

“Mun birne mutane takwas, sannan wasu mutane shida su na jinya a asibiti.” Inji Alhaji Iliyasu Sulaiman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel