Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

- Najeriya ta sake samun labari mara dadi daga bankin duniya

- A cewar bankin, Najeriya aka fi yawan mutane marasa wutan lantarki

- Bankin ya kara da cewa yan kasuwa na asarar kudi sakamakon rashin isasshen wutan lantarki

Yan Najeriya da yan kasuwa na wahala sakamakon rashin isasshen wutan lantarki a kasar.

Bankin duniya ya ce yan kasuwa na asarar $29bn a shekarar sakamakon wannan matsalar da Najeriya ke fama da ita.

A cewar rahoton Punch, babbar bankin ya ce Najeriya aka fi yawan adadin mutane marasa wutan lantarki.

Musamman, a rahoton shirin farfado da sashen wutan lantarki na bankin, cikin kowani mutane 10 marasa lantarki a duniya, daya dan Najeriya ne, TheCable ta kara.

DUBA NAN: Mafi yawancin Gwamnonin dake kan madafun iko sun fito ne daga wannan jami'ar

Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya
Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya Photo: @dheenylkhair
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin Arewacin Najeriya

Bankin yace: "Cikin kowani Naira goma da ake biyan kamfanonin raba wutar lantarki, ana asaran N2.60 sakamakon rashin kayan aikin kwarai da barayin wuta kuma ana ba N3.40 ba kwastamomi ke biya ba."

"Kashi 60 cikin 100 na kwastamomi ba su da mita, kuma ana zaluntarsu idan aka raba Bill. Hakan ya sa mutane ke kin biyan kudin wuta."

Bugu da kari, bankin yace ko kudin tallafin da gwamnati ke biya na wutan lantarki masu kudi ke amfana.

An kara da cewa: "Masu kudi sun fi amfani da wuta; saboda haka su suka fi jin dadin taimakon tallafin alhalin basu bukata."

A wani labarin kuwa, Hukumar tara kudaden shiga na jihar Kaduna, KADIRS, ta kulle hedkwatar hukumar rarraba lantarki na jihar Kaduna (Kaduna Electric) kan kin biyan haraji da ya kai Naira miliyan 464, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar ta shafinta na Twitter ta ce tun daga shekarar 2012 zuwa 2018 ne aka ki biyan harajin.

Sai dai mahukunta hukumar lantarkin na Kaduna ba ta ce komai ba game da batun kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng