Masu son ganin bayan Pantami makiyan Arewa ne, Kungiyoyin Arewa maso gabas

Masu son ganin bayan Pantami makiyan Arewa ne, Kungiyoyin Arewa maso gabas

- Wata kungiyar Arewa ta ce wasu makiyan Arewa ke kokarin ganin bayan Dr Isa Pantami

- A cewar kungiyar, masu kira ga Pantami yayi murabus basu da kwakkwaran hujja

- Kawai bakin ciki ne da hassadan Najeriya da jama'arta, cewar kungiyar

Gamayyar kungiyoyin Arewa maso gabas ta alanta cewa masu son ganin bayan ministan sadarwa da tattalin arzikin zaman, Dr Isa Ali Pantami, makiyan Arewacin Najeriya ne.

Kungiyar ta tuhumi gidajen jaridun Najeriya da rashin daidaito wajen bayar da rahotanninsu kan Ministan.

A jawabin da shugaba da sakataren gamayyar, Abubakar Modire da Shuaibu Gidado, suka rattafa hannu, kungiyar ta ce wasu sun lashi takobin ganin sun ga bayan Ministan.

A cewar jawabin yadda Vanguard ta gani: "Masu sharrin nan da suka gaza gabatar da wani hujja kan zarge-zargen da suke masa sun kara da bakin cikin dukkan al'ummar Arewa, musamman matasanta."

"Mun lura cewa an bada wannan kwangilar ne ga wasu gidajen jarida makiya Arewa."

DUBA NAN: Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Masu son ganin bayan Pantami makiya Arewa ne, Kungiyoyin Arewa maso gabas
Masu son ganin bayan Pantami makiya Arewa ne, Kungiyoyin Arewa maso gabas Credit: @FMoCDE
Asali: Twitter

DUBA NAN: Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

A bangare guda, a yayin da mutane da kungiyoyi da dama ke neman cewa ganin Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami ya yi murabus saboda alaƙanta shi da goyon bayan Taliban, Hukumar Yan Sandan Farar Hula, DSS ta yi watsi da kalaman tsohon direktan ta, Denise Amachree, kan rahoton da ta miƙa wa gwamnatin Buhari.

Amachree, tsohon mataimakin direkta a DSS ya yi ikirarin cewa ƴan sandan farar hular sun sanar da gwamnatin tarayya da Majalisar Tarayya kan tsauraran ra'ayoyin Pantami na goyon bayan Taliban kafin tabbatar da naɗinsa a matsayin minista a 2019, Vanguard ta ruwaito.

Amachree ya kuma ce ministan ya yi murabus saboda yana da wahala mutum mai irin tsatsaurar ra'ayi irinsa ya canja tunani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel