Ra'ayinsa kawai ya faɗa, DSS ta yi watsi da furucin DG a kan Pantami

Ra'ayinsa kawai ya faɗa, DSS ta yi watsi da furucin DG a kan Pantami

- Hukumar Yan sandan farar hula, DSS, ta nesanta kanta daga kalaman tsohon direktan ta Mr Denise Amachree

- Amachree, ya yi ikirarin cewa DSS ta sanar da gwamnatin Buhari game da tsatsauran ra'ayoyin Pantami kafin a naɗa shi minista

- Amma kakakin DSS, Afunanya Peter ya ce tsohon direktan ya faɗi ra'ayin kansa ne kawai kuma ba shi ke yin magana a madadin hukumar ba

A yayin da mutane da kungiyoyi da dama ke neman cewa ganin Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami ya yi murabus saboda alaƙanta shi da goyon bayan Taliban, Hukumar Yan Sandan Farar Hula, DSS ta yi watsi da kalaman tsohon direktan ta, Denise Amachree, kan rahoton da ta miƙa wa gwamnatin Buhari.

Amachree, tsohon mataimakin direkta a DSS ya yi ikirarin cewa ƴan sandan farar hular sun sanar da gwamnatin tarayya da Majalisar Tarayya kan tsauraran ra'ayoyin Pantami na goyon bayan Taliban kafin tabbatar da naɗinsa a matsayin minista a 2019, Vanguard ta ruwaito.

Ra'ayinsa kawai ya faɗa, DSS ta yi watsi da furucin DG a kan Pantami
Ra'ayinsa kawai ya faɗa, DSS ta yi watsi da furucin DG a kan Pantami. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sunayen sabbin alƙalai 18 da Buhari ya amince da naɗinsu a kotun daukaka ƙara

Amachree ya kuma ce ministan ya yi murabus saboda yana da wahala mutum mai irin tsatsaurar ra'ayi irinsa ya canja tunani.

Ya ce DSS na da bayani kan duk wasu mutane da ta kama a sa ido a kansu, inda ya kara da cewa sun sanar da FG da Majalisar Tarayya tsatsauran ra'ayin da Ministan ke da shi a baya.

"Babu wani bayani da DSS bata sani ba. Mun san komai. A lokacin da na ke aiki a can, muna da bayanai kan duk wani mutum da akwai bukatar a yi bincike a kansa," in ji Amachree.

"Lokacin bincike kan duk wani da za a naɗa minista ko kwamishina ko wani muƙami, a kan tura wa DSS sunan ka. Za su yi bincike kan asalin ka har kakanka sai sun bincika.

"Za su duba makarantun da ka yi har zuwa frimare. Kuma za su rika bibiyar abin da ka ke yi a Intanet da ma sauran harkokin ka na yau da kullum. Mun samu bayanai da yawa kuma ina tabbatar maka mun san da batun Pantami."

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

Amma, DSS a ranar Alhamis ta nesanta kanta daga ra'ayoyin da tsohon direktan ya bayyana, ta yi ikirarin cewa wannan ra'ayin kansa ne kawai ya faɗa kuma baya wakiltar hukumar.

Kakakin DSS, Ifunanya Peter, wanda ya fitar da sanarwar ya ce Amachree ya fadi ra'ayinsa ne ba matsayar DSS ba.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel