Yau za'ayi jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi

Yau za'ayi jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi

- Komai ya kankama don gudanar da jana'izar tsohon shugaban Chadi, Idriss Deby

- Manyan shugabannin kasashen duniya zasu halarci taron a N'Djamena

- An sanar da mutuwar Deby ne ranar Talata

Kasar Chadi za ta bizne tsohon shugabanta, Idriss Deby Itno a ranar Juma'a, 23 ga watan Afrilu 2021, bayan kisansa da yan tawayen FACT sukayi a batakashi da sukayi a farkon mako.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, zai halarci taron jana'izar tare da dinbin shugabannin kasashe na Afrika.

Hakazalika shugaban harkokin wajen kasashen Turai, Josep Borrell, zai halarci jana'izar.

An shirya fara taron jana'izar ne da safe a farfajiyar La Place de la Nation, dake N'Djamena.

Bayan haka za'a yi masa Sallah a babban Masallacin kasar sannan a bizneshi a kauyen Amdjarass, inda aka birne mahaifinsa, a gabashin sahara kusa da kasar Sudan.

KU DUBA: Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

Yau za'ayi jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi
Yau za'ayi jana'izar Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasar Chadi

KU KARANTA: Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Mun kawo muku rahoton cewa shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya riga mu gidan gaskiya, bayan samun nasara a zaben kasar.

Rahotanni sun nuna cewa Idris Deby ya mutu ne sakamakon harbin da akayi masa a faggen yaki da yan tawaye. An saki sakamakon nasararsa a zaben ne ranar Litnin.

Idris Deby ya mutu yana mai shekaru 68.

Bayan mutuwar mahaifinsa a filin daga, hukumar Sojin kasar Chadi ta alanta nadin 'dan marigayi, Mahamat Kaka, a matsayin mukaddashin shugaban kasar.

Kakakin hukumar Sojin Chadi ya sanar. Mahamat Idriss Deby Itno, Janar ne mai tauraro 4 a hukumar Sojin kasar kuma ya nada shekaru 37 da haihuwa.

A cewar Aljazeera, Mahamat Deby zai jagoranci kasar nan na tsawon watanni 18 yayinda majalisar Soji ke shirin gudanar da zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel