Da duminsa: An alanta 'dan Idris Deby, Mahamat Kaka, matsayin mukaddashin shugaban kasar Chadi
- Majalisar Sojin kasar Chadi ta alanta mukaddashin shugaban kasar
- Wannan ya biyo bayan sanar da kisan shugaban kasar, Idris Deby, ranar Talata
- Mahamat na daya daga cikin 'yayan marigayin kuma babban jami'in sojan kasar
Bayan mutuwar mahaifinsa filin daga, hukumar Sojin kasar Chadi ta alanta nadin 'dan marigayi, Mahamat Kaka, a matsayin mukaddashin shugaban kasar.
Kakakin hukumar Sojin Chadi ya sanar.
Mahamat Idriss Deby Itno, Janar ne mai tauraro 4 a hukumar Sojin kasar kuma ya nada shekaru 37 da haihuwa.
A cewar Aljazeera, Mahamat Deby zai jagoranci kasar nan na tsawon watanni 18 yayinda majalisar Soji ke shirin gudanar da zabe.
KU KARANTA: Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna
Mun kawo muku rahoton cewa shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya riga mu gidan gaskiya, bayan samun nasara a zaben kasar.
Rahotanni sun nuna cewa Idris Deby ya mutu ne sakamakon harbin da akayi masa a faggen yaki da yan tawaye.
An saki sakamakon nasararsa a zaben ne ranar Litnin.
Idris Deby ya mutu yana mai shekaru 68.
Ya hau mulkin kasar bayan tawaye a shekarar 1990. Ya lashe kashi 79.3% na zaben da aka gudanar ranar 11 ga Afrilu.
Ya kwashe shekaru 30 yana mulki.
DUBA NAN: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC
Asali: Legit.ng