Gwamnatin kasar Chadi ta bude iyakokinta bayan kwana daya da rufewa

Gwamnatin kasar Chadi ta bude iyakokinta bayan kwana daya da rufewa

- Da alamun abubuwa sun fara daidaituwa a kasar Chadi bayan kisan shugabanta

- A jiya Sojoji sun ce ba za'a bude iyakoki ba sai lokacin da ya hali yayi

- Najeriya na da iyaka da kasar Chadi, a jihar Borno

Chadi ta bude iyakokin ranar Laraba, kwana daya bayan rufe iyakokin sakamakon kisan shugaban kasa Idrs Deby Itno, a faggen yaki da yan tawaye.

Kakakin majalisar sojojin kasar, Azem Bermandoa Agouna, a ranar Talata ya sanar da rufe iyakokin.

Gwamnatin kasar Chadi ta bude iyakokinta bayan kwana daya da rufewa
Gwamnatin kasar Chadi ta bude iyakokinta bayan kwana daya da rufewa

KU KARANTA: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby

Mun kawo muku labarin cewa Majalisar Sojojin kasar Chadi ta alanta kafa dokar hana fita da kuma kulle dukkan iyakokin kasar

Bidiyon Aljazeera na jawabin majalisar Sojin ya nuna mambobin majalisar suna sanarwa

Hakazalika, majalisar ta rusa majalisar dokokin kasa, hakazalika kundin tsarin mulkin kasar. Dokar hana fita zai fara ne daga karfe 6 na yamma zuwa 5 na Asuba.

Jawabin yace: "An rusa majalisar dokokin tarayya da gwamnati, shugaban majalisar Sojoji zai kafa kwamitin rikon kwarya, an saka dokar ta baci a dukkan yankunan kasar."

"An rufe iyakokin kasar har zuwa lokacin da za'a kafa sabbin dokoki, za'a nada gwamnatin da zata shirya sabon zabe, za'a kafa sabbin hukumomin da zasu taimaka wajen gudanar da zaben lumana."

DUBA NAN: Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel