An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta baci a Chadi

An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta baci a Chadi

- Ba tare da wata-wata ba, hukumar Sojojin Chadi ta dau ragamar mulkin kasar

- Wannan ya biyo bayan rusa kundin tsarin mulkin kasar da majalisa

- A tsarin doka, Kakakin majalisar dokoki ya kamata a baiwa shugabancin kasa

Majalisar Sojojin kasar Chadi ta alanta kafa dokar hana fita da kuma kulle dukkan iyakokin kasar bayan sanar da mutuwar shugaban kasa, Idris Deby Itno, ranar Talata.

Majalisa ta rufe iyakokin kan tudu, ruwa da sararin samaniya har sai lokacin da hali yayi.

Bidiyon Aljazeera na jawabin majalisar Sojin ya nuna mambobin majalisar suna sanarwa.

Hakazalika, majalisar ta rusa majalisar dokokin kasa, hakazalika kundin tsarin mulkin kasar.

Dokar hana fita zai fara ne daga karfe 6 na yamma zuwa 5 na Asuba.

DUBA NAN: Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna

An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta bace a Chadi
An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta bace a ChadiPHOTO: MARCO LONGARI / AFP
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC

Jawabin yace: "An rusa majalisar dokokin tarayya da gwamnati, shugaban majalisar Sojoji zai kafa kwamitin rikon kwarya, an saka dokar ta baci a dukkan yankunan kasar."

"An rufe iyakokin kasar har zuwa lokacin da za'a kafa sabbin dokoki, za'a nada gwamnatin da zata shirya sabon zabe, za'a kafa sabbin hukumomin da zasu taimaka wajen gudanar da zaben lumana."

Bayan mutuwar mahaifinsa filin daga, hukumar Sojin kasar Chadi ta alanta nadin 'dan marigayi, Mahamat Kaka, a matsayin mukaddashin shugaban kasar.

Kakakin hukumar Sojin Chadi ya sanar.

Mahamat Idriss Deby Itno, Janar ne mai tauraro 4 a hukumar Sojin kasar kuma ya nada shekaru 37 da haihuwa.

cewa shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya riga mu gidan gaskiya, bayan samun nasara a zaben kasar.

Hukumar ta ceIdris Deby ya mutu ne sakamakon harbin da akayi masa a faggen yaki da yan tawaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel