Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna

Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna

- Duk da gargadin El-Rufa'i, iyayen daliban FCFM sun biya kudin fansa

- Iyayen ce masu garkuwa da 'ya'yansu suna neman N500m

- Kawo yanzu an sako dalibai 10 cikin 39 da aka sace a makarantar FCFM

Iyayen dalibai 39 da aka sace a kwalejin FCFM Afaka Kaduna sun ce sun biya milyan 17 don sakin dalibansu amma yan bindigan mutum 10 kawai suka saki cikinsu.

A binciken da Jaridar Leadership tayi ikirarin gudanarwar, iyayen daliban sun biya kudin ne don a sake musu yaransu gaba daya amma goma kadai yan bindigan suka saki.

Wani mahaifi wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace, "yan bindigan sun yarda zasu saki yaranmu idan muka biyasu kudin, sai muka tara muka biyasu amma mutum goma kadai suka saki."

"Mun hada kai ne da wasu tsaffin yan bindiga wadanda ke tayamu ciniki da wadanda suke rike da yaranmu, an kawo su daga Ilori kuma aka biyasu kudin aikinsu."

"Mun baiwa tsaffin yan bindigan N17 million don baiwa wadanda ke rike da yaranmu amma mutum 10 kadai suka saki. Suna bukatan karin kudi ko su kashe yaran."

Wannan bayani na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada cewa ba zata biya kudin fansan daliban ba.

KU KARANTA: An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta baci a Chadi

Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna
Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matsalar tsaro da Rashin hanyoyi masu kyau: Ahmed Musa ba zai buga wasannin 'Away' ba, Kano Pillars

Iyayen daliban kwalejin sun ce an bukaci su biya kudin fansar 'ya'yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su.

An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan 'ya'yansu, Vanguard ta wallafa.

Duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng