Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari garuruwa biyu a Zamfara

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari garuruwa biyu a Zamfara

- Yan bindiga sun afka wa mutanen kauyukan Yar Doka da Kongo

- Mazauna garin sun ce a safiyar yau ne maharan suka iso garin suna harbe-harbe

- Yan Sakai sun yi kokarin dakile harin yan bindiga amma ba su yi nasara ba

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a halin yanzu sun kai hari kauyukan Yar Doka da Kongo a yankin Magami da ke karamar hukumar Gusau na jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna kauyukan sun ce yan bindigan da yawa sun afka musu a safiyar ranar Laraba suka bude musu wuta.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari garuruwa biyu a Zamfara
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari garuruwa biyu a Zamfara. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa

A baya, mazauna kauyen Yar Doka sun taba yin hijira sun fice daga gidajensu bayan wani mummunan hari da yan bindigan suka kai musu watanni kadan da suka gabata.

"Sun kai hari a garin suka kona musu kayan abinci.

"Mazauna garin sun tsere sun tafi garin Magami mai nisan kilomita 7 yamma da su.

"Kwanan nan suka dawo ashe ba su san yan bindigan suna shirin sake kawo musu hari ba.

"Yanzu suna nan suna yawo daga kauye zuwa kauye.

"Na ga mutane da dama da suka jikkata ana kai su asibitoci.

"Yan banga da aka fi sani da Yan Sakai sun tafi garin Yar Doka domin dakile harin amma dole suka dawo saboda makaman maharan ya fi nasu," a cewar wani mazaunin garin mai suna Babangida.

KU KARANTA: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

An yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu kan lamarin amma ba a same shi ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel