Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa

Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa

- Alhaji Ali Sarkin Mota, Direban Firimiyan arewa, Sir Ahmadu Bello ya riga mu gidan gaskiya

- Ali Sarkin Mota ya rasu a safiyar ranar Laraba a asibiti a Kaduna bayan fama da jinya

- Za a yi jana'izarsa a babban masallacin Sultan Bello da ke Kaduna bayan sallar Azahar

Alhaji Ali Sarkin Mota, direban Sardaunan Sokoto Firimiyan arewa Sir Ahmadu Bello ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu yana da shekaru 98 a duniya.

Wasu makwabtan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a asibiti a safaiyar ranar Laraba bayan jinya, Daily Trust ta ruwaito.

Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa
Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa. Hoto: @BBCHausa
Asali: Twitter

Iyalansa sun bada sanarwar cewa za a yi jana'izarsa a yau Laraba bayan sallar Azahar a masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki a garin Kaduna.

DUBA WANNAN: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

Ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki masu yawa.

A baya bayan nan ne Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya karrama Ali Sarkon Mota yayin bikin cika shekaru 50 da kafa Arewa House a Kaduna.

Yayin taron, Sultan ya bukaci manyan baki da masu ruwa da tsaki a wurin taron da su karrama Ali Sarkin Mota, sannan dattijon ya rika bi wuri-wuri yana gaisawa da manyan baki a wurin taron.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Kaduna, Jigawa, Kebbi da Ekiti kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Kotun shari'ar ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Saura sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, Ministan Muhalli Mohammed M. Abubakar da ministan Harkokin Yan sanda, Mai gari Dingyadi dss.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel