Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

- Wata matar aure a jihar Zamfara ta roƙi kotun Shari'a ta raba aurenta da mijinta saboda girmar mazakutarsa

- Hakan na zuwa ne kimanin mako guda da ɗaura aurensu bayan mijin ya kusance ta sau biyu kuma ta gane ba za ta iya jurewa ba

- A ɓangarensa mijin matar shima ya amince kotu ta raba auren tunda matar ta nuna ba za ta iya cigaba da zama da shi ba

Wata mata ƴar Nigeria da bata daɗe da aure ba ta roƙi kotun Shari'a da ke Samaru, Gusau, jihar Zamfara ta raba aurensu bayan sati ɗaya saboda girman mazakutar mijin.

The Nation ta ruwaito cewa A'isha Dannupuwa, mai ƴaƴa uku ta shaidawa kotu cewa ta auri mijinta na biyu ne bayan auren ta na farko ya mutu.

Ba zan iya da zama da shi ba saboda girman mazakutarsa, matar aure ta faɗawa kotu a Zamfara
Ba zan iya da zama da shi ba saboda girman mazakutarsa, matar aure ta faɗawa kotu a Zamfara. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

KU KARANTA: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

A jawabinta, ta ce al'adarsu ne dama ta fara tarewa a gidan iyayensa kafin daga baya ta tare a gidan mijinta, bayan ɗaurin aure.

"Da ya zo, ya kusance ni amma a maimakon samun natsuwa sai akasin haka ta faru saboda tsabar girman mazakutarsa," ta shaidawa kotu.

A'isha Dannupuwa ta shaidawa kotu cewa tun lokacin ta riƙa fama da ciwo a gabanta hakan yasa ta sha wasu magungunan gargajiya da mahaifiyarta ta haɗa, inda ta bata tabbacin cewa za ta saba.

DUBA WANNAN: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

"Bayan kwanaki biyu, ya sake kawo ziyara, ya sake kusanta ta amma ba zan iya jurewa ba. Daga nan ne na san ba zan iya cigaba da auren ba saboda girmar mazakutarsa," ta ƙara da cewa.

A ɓangarensa mijin bai musanta abin da matarsa ta shaidawa kotun ba inda shima ya amince a raba auren nasu na mako ɗaya.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel