An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano

An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano

- An ceto wata yarinya da iyayenta suka rufe ta a daki na tsawon shekaru 10 a Kano

- Bincike ya nuna cewa iyayen sun kulle yarinyar ne tun tana da shekaru 5 a duniya

- Tuni dai an garzaya da yarinyar zuwa asibiti domin duba lafiyarta yayin da yan sanda suke kama mahaifyarta

Yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano
An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano. Hoto: Rundunar Yan sandan Kano
Asali: Twitter

An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano
An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano. Hoto: Rundunar Yan sandan Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun ji 'ba daɗi' a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talat ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Kiyawa ya ce an tafi da Aisha asibitin Kwararru na Murtala Mohammed a Kano domin likitoci su duba lafiyarta.

An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano
An ceto yarinyar da iyayenta suka garƙame tsawon shekaru 10 a ɗaki a Kano. Hoto: Rundunar Yan sandan Kano
Asali: Twitter

Yan sandan sun ce an samu yarinyar cikin yanayi mara dadi na tsananin yunwa da bukatar kula duba da irin halin da aka same ta a wurin da aka kulle ta.

Rahotanni sun nuna cewa iyayen yarinyar sun rufe ta ne a dakin tun lokacin tana yar shekara biyar.

KU KARANTA: An cafke wasu mutum biyu da ke yi wa ƴan bindiga aikin 'likitanci' a Kaduna

Mai magana da yawun yan sandan ya ce an tura batun sashin binciken manyan laifuka, sannan idan an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: