Ku nisanci jihar Ebonyi, Gwamna Umahi ya yi kira ga Fulani makiyaya

Ku nisanci jihar Ebonyi, Gwamna Umahi ya yi kira ga Fulani makiyaya

- Ku yi kaura daga jihar Ebonyi na dan lokaci, David Umahi ga Fulani Makiyaya

- Kungiyar Miyetti Allah ta yi tsokaci kan zargind a ake yiwa makiyaya na kashe mutane a Ebonyi

- Gwamnan Ebonyi ya ce Makiyaya sun basa kunya duk da abubuwan da yake na karesu

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya yi kira ga Fulani Makiyaya da su nisanci jiharsa yanzu.

Gwamnan ya bada wannan umurni ne yayin hira da manema labarai bayan zaman majalisar zantarwan jihar, ranar Talata, rahoton Daily Trust.

Ya ce a yanzu, babu makiyayi ko guda a jihar sakamakon tashin hankalin da ake ciki.

Gwamna, wanda ya yi All-wadai da kisan yan sanda da kona ofishin yan sanda a yankin Igbo, ya bukaci makiyaya su nisanci jihar har sai abubuwa sun yi sauki.

Ya kara da cewa shugabannin yankin Igbo su tashi tsaye su yi Alla-wadai da Kashe-kashen dake faruwa.

"Muna kashe yan sanda, muna kona ofishoshin yan sanda saboda haka shugabannin yankin su fahimci cewa matsalarmu ba makiyaya bane kawai. Babu makiyayi ko guda a jihar Ebonyi yanzu," yace.

"Bamu koresu ba. Da kansu suka tafi, hakan na nufin cewa sun san hare-haren da ake kaiwa a jihar Ebonyi."

"Akwai tashin hankali. Mun turawa Miyetti Allah sakonni cewa akwai tashin hankali a Ebonyi kuma zamu so su nisanci jihar har sai abubuwa sun yi sauki a jihar."

DUBA NAN: Majalisar dattawa ta amince Buhari ya sake cin bashin sama da Tiriliyan 1

Ku nisanci jihar Ebonyi, Gwamnan Ebonyi ya yi kira ga makiyaya
Ku nisanci jihar Ebonyi, Gwamnan Ebonyi ya yi kira ga makiyaya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Akwai masu shirin jefa yankin Igbo cikin yaki, Gwamnan jihar Ebonyi

A bangare guda, shugabannin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na yankin kudu maso yamma sun umurci mambobinsu suyi kaura daga jihar Ebonyi sakamakon kashe-kashen da akayi kwanakin nan.

An zargi Fulani Makiyaya da laifin kisan mutane akalla 15 a karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi a makon da ya gabata.

Kungiyar Miyetti Allah idan mambobinta sukayi kaura na dan lokaci, za'a samu zaman lafiyan da zai bawa jami'an tsaro daman gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel