Mun umurci Makiyaya suyi kaura daga jihar Ebonyi, Kungiyar Miyetti Allah

Mun umurci Makiyaya suyi kaura daga jihar Ebonyi, Kungiyar Miyetti Allah

- Kungiyar Miyetti Allah ta yi tsokaci kan zargind a ake yiwa makiyaya na kashe mutane a Ebonyi

- Gwamnan Ebonyi ya ce Makiyaya sun basa kunya duk da abubuwan da yake na karesu

- An kaddamar bincike kan rayuka 15 da aka salwantar a jihar

Shugabannin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na yankin kudu maso yamma sun umurci mambobinsu suyi kaura daga jihar Ebonyi sakamakon kashe-kashen da akayi kwanakin nan.

An zargi Fulani Makiyaya da laifin kisan mutane akalla 15 a karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi a makon da ya gabata.

Kungiyar Miyetti Allah idan mambobinta sukayi kaura na dan lokaci, za'a samu zaman lafiyan da zai bawa jami'an tsaro daman gudanar da bincike.

Mun umurci Makiyaya suyi kaura daga jihar Ebonyi, Kungiyar Miyetti Allah
Mun umurci Makiyaya suyi kaura daga jihar Ebonyi, Kungiyar Miyetti Allah
Asali: Twitter

KU KARANTA: Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

Shugabann Miyetti Allah na yankin, Gidado Siddiki, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Laraba a Awka, babbar birnin jihar Anambara.

Siddiki yace, "Mun bada umurni dukkan makiyaya su fita daga jihar yanzu. Muna tsoron kada a kashesu da sunan ramuwar gayya. Shi yasa muka umurcesu su yi kaura daga jihar yanzu kuma su dawo idan abubuwa sukayi sauki."

"Akwai takaici saboda Fulani Makiyaya sun yi shekara da shekaru a wajen kuma suna zaman lafiya da mutan garin."

Siddiki ya yi kira ga Makiyaya dake yankin kada su dau doka a hannunsu.

KU KARANTA: An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

A bangare guda, Ndinne Igbo, wata kungiyar zamantakewar mata, ta yi barazanar cewa mambobinta za su yi tattaki tsirara a fadin kasar ta Igbo don nuna rashin amincewa da kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankin idan har hukumomin da abin ya shafa ba su shawo kan lamarin ba.

Yankin kudu maso gabas na fama da rikice-rikicen makiyaya a makwannin da suka gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da harin makiyaya da ya auku a jihohin Enugu da Ebonyi, inda ta koka kan yadda yara ‘yan kabilar Ibo da dama suka zama cikin mummunan harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng