Akwai masu shirin jefa yankin Igbo cikin yaki, Gwamnan jihar Ebonyi

Akwai masu shirin jefa yankin Igbo cikin yaki, Gwamnan jihar Ebonyi

- Gwamnonin Jihohin Kudu maso gabas sun yi zama a kan sha’anin tsaro

- Gwamnan Ebonyi wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Ibo ya yi watsi da hukumar ESN da IPOB ta kafa

- Wannan ya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa ofishoshin yan sanda a yankin

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa wasu mutane na kokarin jefa yankin Kudu maso gabas (yankin Igbo) cikin yaki.

Magana yayin hira da ChannelsTV, Umahi ya ce wasu yan bindiga ke tayar da tarzoma suna kashe mutane da sunan yan kungiyar IPOB.

Duk da cewa bai ambaci sunayen wadanda yake zargi ba, ya yi gargadin cewa gwamnonin yankin ba zasu zuba ido a jefasu cikin rudani ba.

"Abinda wasu mutane ke yi shine jefa kudu maso gabas cikin yaki sannan su gudu, kuma ba zamu yarda da haka ba, ba zamu yarda a sake yaudaranmu ba," yace.

"Mutane su bi a hankali, kuma su sani cewa akwai wani shiri da wasu marasa kishin yankin kudu maso gabas keyi, na jefamu cikin yaki kuma mun waye yanzu."

Gwamnan Umahi ya ce sabon hukumar tsaro, Ebube Agu, da suka kafa ne kadai sanannen hukumar tsaron a yankin.

KU DUBA: Babu kudi a Najeriya, sai da aka buga sabbin kudi N60bn aka raba mana a watan Maris, Gwamna Obaseki

Ana shirin jefa yankin Igbo cikin yaki, Gwamnan jihar Ebonyi
Ana shirin jefa yankin Igbo cikin yaki, Gwamnan jihar Ebonyi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Yobe an angwance da diyar marigaryi Abacha, Hajiya Gumsu

Kun ji cewa jihohin kudu maso gabas sun kafa jami’an tsaronsu na musamman a dalilin matsalolin da ake fuskanta na rashin tsaro a ‘yan kwanakin nan.

Legit.ng Hausa ta samu rahoto cewa an sa wa wadannan jami’an tsaro da aka kafa suna da EBUBEAGU.

An dauki wannan mataki ne bayan gwamnonin yankin da sauran masu ruwa da tsaki sun yi wani zama na musamman a jihar Imo a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng