Ganduje ya kaddamar da babura na musamman don dakile cinkoso a Kano

Ganduje ya kaddamar da babura na musamman don dakile cinkoso a Kano

- Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabbin babura a Kano na hukumar KAROTA

- Hukumar ta KAROTA ta ce wannan baburan za su taimakawa jami'an hukumar wurin kama masu laifi da dakile masu shigo da haramtattaun kaya Kano

- Baffa Dan'agundi, shugaban KAROTA, ya ce da kudaden da aka samu bayan korar jami'an bogi aka siya baburan

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da babura na musamman guda 25 da hukumar rage cinskoso na jihar, KAROTA, ta siyo domin dakile cinkoso a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke kaddamar da baburan a ranar Lahadi a Kano, Ganduje ya za a yi amfani da babburan ne somin tabbatar da cewa masu ababen hawa sun bi doka a kasa.

Ganduje ya kaddamar da babura na musamman don dakile cinkoso a Kano
Ganduje ya kaddamar da babura na musamman don dakile cinkoso a Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC

Ya ce baburan za su bawa jami'an KAROTA damar rasta wurare cikin gagawa domin sanya ido kan yadda masu saba dokokin tuki da gano masu shigo da haramtattun ababe zuwa jihar.

Gwamnan ya bukaci jami'an na KAROTA su zage damtse a kokarinsu na kula da cinkoson ababen hawa da kama masu saba doka.

Ya kuma bukaci su tabbatar an rika kama wadanda ke shigowa da haramtattun ababe zuwa jihar.

Ganduje ya yabawa shugaban KAROTA, Baffa Dan'agundi saboda bullo da wannan sabuwar tsarin.

Tunda farko, Dan'agundi ya ce an siyo baburan ne da kudaden da aka samu bayan korar ma'aikatan bogi a hukumar.

KU KARANTA: Fusatattun ma'aikata sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan Nasarawa

"Wasu lokutan, muna ganin abubuwa da dama suna faruwa, muna ganin miyagu suna daukan haramtattun abubuwa cikin motocci amma babu motoccin da za mu bi su zuwa wurin da za su tafi mu kama su.

"Amma, da wannan sabbin baburan, za mu iya kama masu laifi da dama," Dan'agundi ya bawa gwamnan tabbaci.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel