Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC

Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC

- Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan Imo ya ce wani gwamnan kudu, sarki da tsohon sanatan arewa suka fito da shi daga hannun EFCC

- Hukumar ta EFCC ta tsare Okorocha na kimanin awanni 48 a ofishinta tana masa tambayoyi kan zarginsa da almundahanar kudi yayin da ya ke gwamna

- Okorocha, cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar ya bukaci gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya dena fada da shi

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a ranar Lahadi ya ce bayyana cewa wani gwamna daga kudu maso kudu, sarki da tsohon sanata daga arewa ne suka tabbatar hukumar EFCC ta sako shi, The Punch ta ruwaito.

Okorocha, cikin sanarwar da kakakinsa Sam Onwuemeodo ya fitar a ranar Lahadi ya bukaci gwamnan jihar Hope Uzodinma ya dena fada da mai gidansa.

Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC
Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC. Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Fusatattun ma'aikata sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan Nasarawa

Sanarwar ta kara da cewa Uzodinma ya karbe aikin kakakin hukumar EFCC a binciken da hukumar ke yi a kansa (shi Okorocha).

Onwuemeodo ya ce kalaman da hadimin Uzodinma Modestus Nwamkpa ya fitar na cewa EFCC ta saki Rochas saboda rashin lafiya ba gaskiya bane.

Wani sashi na sanarwar ta ce, "Bayan kimanin mintuna 45 bayan jami'an EFCC sun kyalle Sanata Rochas Okorocha ya tafi gida bayan shafe awa 48 tare da su, gwamnan Imo Cif Hope Uzodinma ta bakin hadiminsa, Modestus Nwankpa ya fitar da sanarwa kan dalilin da yasa aka kyalle Rochas ya tafi gida.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe Abu-Aisha da wasu manyan kwamandojin ISWAP 17 a Damasak

"Sanarwar ta bawa mutane da dama mamaki kuma akwai alamar tambaya kanta domin ba zai yi wu kakakin EFCC ya bawa Uzodinma damar ya fada dalilin da yasa suka saki daya daga cikin bakonsu ba (Okorocha) bayan ya shafe awa 48 a ofishinsu".

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel