Shugaban Bankin Sterling Ya ɗora alhakin tsallake Najeriya da Tuwita ta yi Kan yan Najeriya

Shugaban Bankin Sterling Ya ɗora alhakin tsallake Najeriya da Tuwita ta yi Kan yan Najeriya

- Shugaban Bankin Sterling ya ce yan Najeriya dakansu ne suka tura tuwita taje Ghana ta gina Hedkwatar ta na Africa saboda halinsu

- Abubakar Sulaiman ya ce masu zuba hannun jari ba zasu zuba dukiyar su a ko ina ba bayan Najeriya

- Sulaiman ya ce Tuwita ta zaɓi Ghana ne kawai amma Kamfanin zaifi maida hankali ga Najeriya

Shugaban bankin Sterling, Abubakar Sulaiman, ya zargi yan Najeriya da laifi kan tsallake Najeriya da kamfanin tuwita ya yi wajen gina hedkwatar sa a Africa.

A kwanan nan ne dai kamfanin tuwita ya bayyana cewa zai gina hedkwatar sa a Africa a ƙasar Ghana.

KARANTA ANAN: UNICEF ta roƙi yan Najeriya da su koma a sake yi musu allurar rigakafin COVID19 karo na biyu

Sai dai ana ganin kamfanin sada zumuntan zaifi maida hankali a Najeriya amma zai gudanar da aikinsa ne daga ƙasar Ghana.

Tuwita ta shirya ɗaukar ma'aikatan ta daga Najeriya a yarjejeniyar yin aiki daga inda suke ba dole sai sun bayyanar da gangar jikinsu ba.

Wannan hukunci da kamfanin tuwita ya yanke na kai ofishinsa Ghana ya baiwa mafi yawan cin yan Najeriya mamaki, inda suka ɗora alhakin hakan kan gwamnati.

Kamfanin tuwita dai ya bayyana dalilinsa na kai hedkwata Ghana. Daga cikin dalilan da daraktocin tuwita suka bayyana akwai; damar yin magana, da kuma demokaradiyya.

Shugaban Bankin Sterling Ya ɗora alhakin tsallake Najeriya da Tuwita ta yi Kan yan Najeriya
Shugaban Bankin Sterling Ya ɗora alhakin tsallake Najeriya da Tuwita ta yi Kan yan Najeriya Hoto: @suleimana
Asali: UGC

A wani jawabi da kamfanin ya fitar, ya ce kasancewar sakateriyar kasuwancin Africa na Ghana, shine ya ƙara ma kamfanin kwarin gwuiwar ya tsallake Najeriya.

KARANTA ANAN: Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari

Duk da waɗannn dalilan da kamfanin ya faɗa, Abubakar Suleiman, ya na ganin laifin yan Najeriya ne.

Ya ce munanan kalaman da yan Najeriya ke yi wajen misalta ƙasar su yasa tuwita tsallake ta wajen gina hedkwatar a Africa.

Ya ce yan Najeriya suyi dai tsammanin komai makamancin wannan saboda yadda suka ɓata ƙasar a idon masu zuba hannun jari.

Suleiman yace: "Da farko kun faɗawa duniya Najeriya cike take da abun tsoro, sannan kunji Tuwita zata gina hedkwata a Ghana Kuma kuna mamakin meyasa haka. Idan har ba zaka iya siyar da kanka ba, babu wanda zai siya."

"Har yau-Har gobe Najeriya itace zuciyar Nahiyar Africa, duk ƙalubalen da muke fuskanta ba dawwamamme bane."

A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Sun sheƙe wasu yan fashin teku 4 a jihar Akwa Ibom

Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta samu nasarar hallaka wasu mutane huɗu da ake zargin yan fashin teku ne.

Kakakin yan sandan jihar ya tabbatar d faruwar lamarin, inda ya ce yan sanda a Marine, ƙaramar hukumar Oron sun fita sintiri ne bayan samu ƙwararan bayanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262