Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami

Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami

- Ministan Sadarwar ƙasar nan, Isa Pantami,ya ƙara jaddada matsayarsa kan kulle duk wani layin waya da ba'a haɗa shi da NIN ba

- Ministan ya faɗi haka ne a wani jerin saƙonni da ya fitar a shafin sa na Tuwita ya yin da yake martani kan wani labarin ƙanzon kurege da ake jingina mishi

- Pantami ya ce gwamnati ta fahimci yan ta'addar sun fara jin zafin kudirin namu tun yanzun, saboda haka babu wata barazana da zata dakatar dashi

Ministan sadarwa na ƙasar nan, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargaɗi yan Najeriya waɗanda har yanzun ba su haɗa layukan wayar su da NIN ba da suyi gaggawar yi.

KARANTA ANAN: Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai

Ministan ya ce babu gudu ba ja da baya, dan haka kowa ya gaggauta haɗa nashi tun kafin lokaci yayi.

Isa Pantami ya faɗi haka ne a wasu zafafan sakonni da ya aike a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita ya yin da yake martani kan zargin da wasu jaridu ke masa da hannu a Boko Haram.

Ministan ya ce babu wasu yan shaci-faɗi da wasu tsirarun mutane za su mishi barazana da shi da zai iya dakatar da shi gudanar da ƙudirin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Babu wani Shaci-Faɗi da zai hana ni sanƙame duk Layukan da ba'a Haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami
Babu wani Shaci-Faɗi da zai hana ni sanƙame duk Layukan da ba'a Haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

A saƙon da ya saki wanda ya yi magana kan NIN, Pantami ya ce:

"Idan baka haɗa layin ka da lambar jikin katin ɗan ƙasa ba wato NIN, to ka gaggauta yi kafin mu ɗauki mataki na gaba. Yan ta'adda sun fara shan wahala da matakin da muka ɗauka."

KARANTA ANAN: Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani

Ya kuma ƙara da cewa ba gudu ba ja da baya kan kudirin gwamnati na sanƙame duk wani layin waya da ba'a haɗa shi da NIN ba don yaƙar matsalar tsaro.

"Akan lamarin haɗa layin waya da NIN don yaƙar rashin tsaro, ba gudu ba ja da baya. Buƙatar mu a ɓangaren gwamnati kamar yadɗa kundin tsarin mulki kasa ya tanadar a sashi na 14 (2) shine samar da tsaro."

"Ba tattalin arziƙi ƙadai muka sa agaba ba, tabbas ba gudu ba ja da baya kuma b wanda ya is ya hana mu, don haka masu ɗaukar nauyin ta'addancin su cigaba," Pantami ya jaddada.

A wani labarin kuma Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi akansa na hannu a Boko Haram

Dr Isa Ali Pantami ya mai da martani kan rubutun wata jarida na cewa yana da hannu a Boko Haram.

Ya yi ishara ga karatuttukansa na sama da shekaru 15 in da yake yakar munanan akidu irin na Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262