Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban tashar jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja daga birnin Landan bayan makonni biyu inda yaje ganin Likita.

Buhari ya dira Abuja ne misalin karfe 5 na yammacin Alhamis, 15 ga Afrilu 2021.

Mun kawo muku rahoton Jaridar Punch na ruwaito cewa komai ya kankama don dawowar shugaba Muhammadu Buhari yau.

Buhari ya tafi Landan tun ranar 30 ga Maris da sunan zuwa duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

A cewar rahoton, an kammala shirye-shiryen tarban shugaban kasa kuma ana kyautata zaton dirarsa Abuja Najeriya yanzu.

Kawo karfe 4 na yamma, Sojoji da yan sanda suna tsaye a kan hanyar tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe zuwa fadar shugaban kasa.

Wannan shine al'adar duk lokacin da shugaban kasan zai wuce ta hanyar.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan
Asali: Twitter

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel