Yanzu-yanzu: Ina kan baka na, sai da gwamnatin tarayya ta buga N60bn don raba mana: Obaseki

Yanzu-yanzu: Ina kan baka na, sai da gwamnatin tarayya ta buga N60bn don raba mana: Obaseki

- Gwamna Obaseki na jihar Edo ya fasa kwai kan kudin da aka raba musu a Maris

- Ministar Kudi, Zainab Shamsuna tace karya ne, babu gaskiya cikin jawabinta

- Obaseki ya mayar da martani, yace gwamnati na kame-kame ne kawai

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ba zai yi cacan baki da gwamnatin tarayya kan maganar da yayi na cewa an buga N60bn a Maris don rabawa gwamnoni.

A ranar Laraba Gwamnatin tarayya ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya marasa tushe da asali.

Ministar kudi da kasafi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana hakan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa ranar Laraba, rahoton TheCable.

A raddin da yayi ga Ministar ranar Alhamis, Obaseki, ta shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa: "Ina da imani hakki ne a kanmu mu bada shawara mai amfani don amfanin kasarmu."

"Kamata yayi Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Shamsuna, ta janyo hankalin yan Najeriya kan irin halin talaucin da kasar ke ciki."

"Maimakon kame-kame, muna kira ga gwamnati ta dau mataki wajen kawo karshen almubazzaranci don dakile tabarbarewan tattalin arzikin kasar."

KU KARANTA:Gwamnan Yobe an angwance da diyar marigaryi Abacha, Hajiya Gumsu

KU KARANTA: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna

Mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.

Gwamnan ya ce kudin wata-wata da ake rabawa gwamnoni bai kai ba, sai da gwamnatin tarayya ta buga sabbin kudi bilyan 50 zuwa 60 aka raba musu.

"Lokacin da aka biyamu kudin wata-wata na Maris, sai da gwamnatin tarayya ta buga N50-N60 billion don kudin su isa a raba mana," Obaseki ya bayyana .

Asali: Legit.ng

Online view pixel