Shugaban Yan Marlian, Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala Alkurani a watan Ramadan

Shugaban Yan Marlian, Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala Alkurani a watan Ramadan

-Abdulaziz Fashola (Naira Marley) ya ba Musulmai wata muhimmiyar shawara a kafar sada zumuntar Twitter

-Mawakin ya bayyana yadda mutum zai kammala Alqurani mai girma cikin watan Ramadan

-Yace mutum zai iya kammala Alkurani idan yana shafi 20 kullum

Mawakin Nigerian nan Abdulaziz Fashola wanda aka fi sani da 'Naira Marley' ya bada wata kyakkyawar shawara ga musulmai a kafar sada zumuntarsa ta Twitter.

Mawakin ya bada shawarar yadda musulmai zasu kammala Alkurani cikin kwaniki 30 na watan Ramadan mai alfarma.

Yace wadanda suke so su kammala karatun Alkuranin zasu rika karanta shafi 20 ne a kullum.

Ya kara da cewa zasu rinka karanta shafi hudu-hudu a bayan kowacce sallar farilla.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Ina kan baka na, sai da gwamnatin tarayya ta buga N60bn don raba mana: Obaseki

Shugaban Yan Marlian a Nigeria, Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala Alkurani a watan Ramadan
Shugaban Yan Marlian a Nigeria, Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala Alkurani a watan Ramadan Hoto: @nairamarley@quransayings Source: Instagram
Asali: Instagram

Ku KURANTA: An bindige yan sanda 3 har lahira a jihar Ebonyi: Rahoto

Dandanan musulmai suka garzaya bangaren sharhi domin bayyana ra'ayinsu:

@yinka cewa yayi: "kayi hakuri amma dole zan fadi wannan, kar kayi wasan zama mutumin kirki, matasa da yawa sun riga sun lalace da wakokinka."

@raihaan yace: "Lallai kam, sharhi akan abin musulunci yafi wanda bana musulunci yawa ba. Kar ka chanza saboda Ramadan, ya kamata kayi amfani da watan azumi ka chanza har abada.

@Inshiirah yace: "Ka samu Alqurani mai fassara ka karanta shi a yaran turanci aya bayan aya bayan kowacce ayar larabci...Zaka karu sosai.

A baya munji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya dukkan musulman kasar nan murnar shigowar watan Ramadan

Shugaban ya shawarci dukkan musulmai da suyi kunnan shegu da duk wadanda suke so su raba kasarnan. ya kuma shawarci musulmai da su ji kan sauran yan uwansu musulmai.

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce an zabe shi ne don bunkasa jihar ba don biyan albashi ba.

Hakan ya biyo bayan sallamar ma'aikata 4000 na kananun hukumomi 23 da suke jihar da gabatar musu da wasikun sallamar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel