Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari

Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari

- Alkali Hadiza Shagari ta babbar kotun tarayya dake Katsina ta yankewa gagararren mai safarar miyagun kwayoyi hukunci

- Kamar yadda kwamandan NDLEA na jihar, Momoudou Sule ya sanar, Ibrahim Ali zai yi shekaru 15 a gidan yari

- Kwamandan ya ja kunnen masu hali irin na Ali, inda yace zasu zakulosu tare da kai su inda ya dace don adana su

Babbar kotun tarayya da ta samu shugabancin Mai shari'a Hadiza Shagari a ranar Laraba, ta yankewa gagararren mai safarar miyagun kwayoyi, Ibrahim Ali, hukuncin shekaru 15 a gidan yari babu tara.

Kafin a kama shi a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, Ali ya kasance mai safara tare da siyar da miyagun kwayoyi a garin Katsina.

A wata tattaunawa da manema labarai da hukumar NDLEA reshen jihar Katsina tayi, kwamandan hukumar, Momoudu Sule, ya sanar da manema labari cewa matashin mai safarar miyagun kwayoyin ya shiga hannu kuma an dinga mishi nasiha kada ya koma ruwa amma a banza.

KU KARANTA: Ku tuhumi magabatana a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya

Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari
Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Facebook

KU KARANTA: Umarnin Ubangiji ne: Fasto yayi zanga-zanga kan mulkin Buhari da akwatin gawa

A yayin da Sule yake kwatanta shekaru 15 a matsayin dogon lokaci, ya ce hakan zai dauke matashin daga titi kuma zai dakile yaduwar miyagun kwayoyi a garin Katsina tare da zama izina ga sauran masu irin halinsa.

"Mun tattara tare da mika shi gaban kotu a watan Nuwamba kuma da izinin Allah an yanke mishi hukunci.

"Ga Allah muke godiya, Ibrahim Ali a halin yanzu zai kwashe shekaru 15 a gidan yari ba tare da biyan tara ba.

"Shekaru 15 sun isa a dauke shi daga titi kuma miyagun kwayooyi zasu ragu a Katsina kuma hakan za ta kasance izina ga wadanda ke da hali irin nashi.

"An yankewa Ibrahim Ali hukunci kuma an kaishi inda ya dace, wato gidan gyaran hali. A don haka nake kira ga wadanda ke irin wannan sana'a da su kara tunani saboda nan jihar Katsina ba wurinsu bane.

“Za mu zo kanku kuma zamu kama ku kuma zamu gurfanar da ku tare da tabbatar da cewakun karba hukuncin da ya dace," Sule yace.

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce an zabe shi ne don bunkasa jihar ba don biyan albashi ba.

Hakan ya biyo bayan sallamar ma'aikata 4000 na kananun hukumomi 23 da suke jihar da gabatar musu da wasikun sallamar.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa an zabe shi ne don samar da damar ayyuka, gina makarantu da asibitoci, gyaran tituna da samar da ma'aikatu don samar da ayyuka na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: