An bindige yan sanda 3 har lahira a jihar Ebonyi: Rahoto

An bindige yan sanda 3 har lahira a jihar Ebonyi: Rahoto

- Gwamnonin Jihohin Kudu maso gabas sun yi zama a kan sha’anin tsaro

- Kuma dai, yan bindiga sun cigaba da kaiwa jami'an tsaro harin kwantan bauna a Abakaliki

- Wannan ya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa matafiya a cikin jihar

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun hallaka jami'an yan sandan Najeriya uku a Abakaliki, birnin jihar Ebonyi da daren Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021.

Yan bindigan sun far kan yan sandan ne a titin Onuebonyi/Nwezenyi misalin karfe 7:30 na dare.

Rahoto ya nuna cewa sun kai harin ne cikin mota kuma suka arce bayan kisan, Inji Leadership.

Wata majiya ta bayyana cewa yan sandan sun samu raunukan harsashi kuma aka sanar da wafatinsu bayan garzayawa da su asibtiin koyarwan jami'ar Alex Ekwueme, dake Abakaliki.

An ajiye gawawwakinsu a asibitin.

DUBA NAN: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi

An bindige yan sanda 3 har lahira a jihar Ebonyi: Rahoto
An bindige yan sanda 3 har lahira a jihar Ebonyi: Rahoto
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa wasu mutane na kokarin jefa yankin Kudu maso gabas (yankin Igbo) cikin yaki.

Magana yayin hira da ChannelsTV, Umahi ya ce wasu yan bindiga ke tayar da tarzoma suna kashe mutane da sunan yan kungiyar IPOB.

Duk da cewa bai ambaci sunayen wadanda yake zargi ba, ya yi gargadin cewa gwamnonin yankin ba zasu zuba ido a jefasu cikin rudani ba.

"Abinda wasu mutane ke yi shine jefa kudu maso gabas cikin yaki sannan su gudu, kuma ba zamu yarda da haka ba, ba zamu yarda a sake yaudaranmu ba," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel