Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma

Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma

- Bisa alamu rikicin jagoranci da ake yi tsakanin Gwamna Makinde da tsohon gwamna Fayose ta zo karshe

- Tsohon mataimakin gwamnan Oyo, Taofeek Arajapa ya kada dan takarar Fayose, Eddy Olafeso a zaben shugabancin PDP na yankin kudu maso Yamma da aka yi ranar Litinin

- Arapaja ya samu goyon bayan Makinde da wasu jiga-jigan yan jam'iyyar na PDP inda ya samu nasarar zama mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (kudu maso yamma)

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Oyo, Taofeek Arapaja ya lashe kujerar shugabancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na yankin Kudu maso Yamma.

An sanar da shi matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya fafata da mataimakin gwamnan jihar Benue, Benson Abounu, The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An ji ƙarar harbe-harben bindiga a yayin da Fayose ke barin wurin taron PDP a Osun

Yanzu-Yanzu: Arapaja ya lallasa Olafeso, ya lashe kujerar shugabancin PDP na Kudu maso Yamma
Yanzu-Yanzu: Arapaja ya lallasa Olafeso, ya lashe kujerar shugabancin PDP na Kudu maso Yamma. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Aparaja, wanda ke bangaran gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya samu kuri'u 343 bayan ya kayarda Dr Eddy Olafeso wanda ya samu kuri'u 330.

Olafeso, yana tare ne da tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose.

Daga bisani Olafeso ya yi na'am da kayen da ya sha kuma ya yi alkawarin aiki tare da Arapaja.

KU KARANTA: Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue

Ya ce:

"Komai ya wuce yanzu, mun bude sabon shafi a jam'iyyar mu. Muna godiya da Allah duk da halin da muka tsinci kanmu, mun bude sabon shafi a jam'iyyar mu. Yanzu ne lokacin. Ina mika godiya ga dukkan wadanda suka mara min baya."

Sabon mataimakin shugaban PDP na kasa (kudu maso yamma) Arapaja, ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Makinde da tsohon gwamna Fayose kan yadda aka gudanar da taron.

Arapaja ya ce:

"Za mu yi aiki tare domin cigaban jam'iyya. Muna sake yi wa jam'iyyar tsari mai kyau. Zan yi aiki tare da dan uwa na Olafeso domin cimma manufofin mu."

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel