Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa

Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa

- Kyaftin din kugiyar Super Eagles Ahmed Musa ya ce zai fara buga wa Kano Pillars wasa

- Tsohon dan wasan na CSKA Moscow ya ce ya tattauna da gwamnan Kano Ganduje kan batun

- Musa ya ce bugawa Kano Pillars wasa sai habbaka darajar League din Nigeria kuma hakan zai bashi damar motsa jiki

Ahmed Musa, kyaftin na kungiyar kwallon kafa na Nigeria, Super Eagles ya ce yana duba yiwuwar komawa kungiyar Kano Pillars na kankanin lokaci, The Cable ta ruwaito.

Tsohon mai bugawa CSKA Moscow gaba baya tare da kowanne kungiya tun bayan rabuwarsa da Al Nassr a watan Oktoban 2020.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An ji ƙarar harbe-harben bindiga a yayin da Fayose ke barin wurin taron PDP a Osun

Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa kungiyar Kano Pillar wasa
Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa kungiyar Kano Pillar wasa. Hoto: @thecableng
Asali: Getty Images

A hirar da ya yi da BBC Sports Africa, Musa ya ce ya yi magana da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano da Shehu Dikko, shugaban kamfanin kula da League, LMC kan yiwuwar bugawa Yaran Masu Gida wasanni kadan.

Tsohon dan wasan na Leicester City ya kuma ce hakan zai taimaka wurin kara fito da gasar na Nigeria a idon duniya sannan zai bashi damar ya rika motsa jiki.

KU KARANTA: Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

"Bayan magana da gwamna da shugaban LMC, Ina duba yiwuwar buga wa Kano Pillars wasu wasanni," in ji Musa.

"Duk abinda zai habaka darajar wasan kwallon kafa a Nigeria abu ne da ya dace in yi kuma Kano pillars na da muhimmin matsayi a zuciya.

"Ita ce kungiyar da ta taimaka min na zama kwararren dan kwallo a yau, don haka akwai alaka mai karfi tsakanin mu fiye da kwallo."

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164