Rashin Tausayi: Wasu Yan bindiga Sun sace Yaro ɗan shekara 13 a jihar Ogun, Sun nemi a biya 50 miliyan

Rashin Tausayi: Wasu Yan bindiga Sun sace Yaro ɗan shekara 13 a jihar Ogun, Sun nemi a biya 50 miliyan

- Wasu yan bindiga da ba'asan ko suwaye ba sun yi awon gaba da wani yaro ɗan kimanin shekara 13 a duniya

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai hari a wani yankin gidaje dake Obada-Odo ranar Asabar da misalin ƙarfe 9 na dare

- Kakar yaron da aka sace ta bayyana cewa yan bindigar sun haɗa da jakukunan su da wayoyin su sannan suka tasa yaron suka tafi da shi

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wani yaro ƙarami ɗan kimanin shekara 13 a Obada-Odo ƙaramar hukumar Ewekoro, jihar Ogun.

KARANTA ANAN: Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai hari a wajen gidajen 'Destiny Estate' dake Obada-Odo ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:15 na dare.

Da zuwan su yankin sai suka fara harbi a iska, kuma suka yi awon gaba da wani yaro mai suna Gbolahan Ajibola, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bayan faruwar lamarin yan bindigar sun nemi iyalan yaron da su biya 50 Miliyan kuɗin fansa kafin su saki yaron daga hannun su.

Rashin Tausayi: Wasu Yan bindiga Sun sace Yaro ɗan shekara 13 a jihar Osun, Sun nemi a biya 50 miliyan
Rashin Tausayi: Wasu Yan bindiga Sun sace Yaro ɗan shekara 13 a jihar Osun, Sun nemi a biya 50 miliyan Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

Lokacin da take bayanin yadda lamarin ya faru, kakar yaron da aka sace, Victoria Felix, tace, yan bindiga shiga sun shigo gidanta a ranar Asabar da daddare.

KARANTA ANAN: 'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Felix ta ce: "Yan bindigar sun faɗo gidanmu ne a lokacin da ni da mahaifiyar yaron muke shiga cikin gidan.

"Sai da na tambayesu meyafaru? Me muka yi muku? Suka umarci mu basu jakunkunan mu, kuma muka basu, suka kwace wayoyin mu.

"Lokacin da suka zo zasu tafi da jikan nawa, na riƙe rigar ɗaya daga cikinsu nace masa su tafi dani ne amma su bar yaron. Amma sai suka buge mu muka faɗi ƙasa suka yi tafiyarsu."

A wani labarin kuma Bayan share shekaru 30 yana mulki, ana sa ran Idris Derby zai sake lashe zabe.

Bayan zama a karagar mulki na tsawon shekaru sama da 30, da alamu Derby zai sake lashe zabe.

A yau ne ake kada kuri'ar zaben shugaban kasa a kasar Chadi, inda ake sa ran lashewar shugaban mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel