Bayan share shekaru 30 yana mulki, ana sa ran Idris Derby zai sake lashe zabe
- Bayan zama a karagar mulki na tsawon shekaru sama da 30, da alamu Derby zai sake lashe zabe
- A yau ne ake kada kuri'ar zaben shugaban kasa a kasar Chadi, inda ake sa ran lashewar shugaban mai mulki
- Wasu daga cikin 'yan takarar sun janye saboda barazana da sue fuskanta daga shugaba Idris Derby
Daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa kan karagar mulki shi ake sa ran zai lashe zabe a wa'adi na shida yayin da masu zabe ke zaben shugaban kasa a kasar Chadi a yau.
Ana zargin Shugaba Idris Derby wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki da aka yi a 1990 da muzgunawa yan adawa gabanin zaben da ake yi.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana wani zalunci da aka yi wa 'yan hamayya da masu zanga-zanga.
KU KARANTA: Cocin Katolika ya gina wa musulmai masallaci a jihar Adamawa
Kungiyar ta ce an yi amfani da karfi a zanga-zangar kin jinin gwamnatin da aka yi a baya-bayan nan.
A cewar wakilin BBC, shugabannin adawa hudu ciki har da Saleh Kebzabo wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa a 2016 sun janye daga takarar saboda zargin hare-haren sojoji.
Sun kuma nemi magoya bayansu su kauracewa zaben kuma su yi zanga-zanga.
KU KARANTA: Minista ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke matukar kaunar kabilar su Jonathan
A wani labarin, Aliko Dangote murnar karin shekara guda a shekarunsa, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya mika sakonsa na fatan alheri ga daya daga cikin manyan masu hannu da shunin na Afirka a cikin wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu.
Shugaban ya bayyana Dangote, wanda ya cika shekaru 64 a ranar Asabar, a matsayin babban abokin tarayya kuma "Jarumin yakin Korona" wanda ya ci gaba da nuna cikakken imani da kasar.
Asali: Legit.ng