An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

- Da yiwuwan aka janye daga yajin aikin Likitoci yau Asabar

- An yi zama na tsawon awanni takwas da wakilan Likitocin ranar Juma'a

- Yau kwanaki tara kenan da kaddamar da yajin aikin Likitocin NARD

Bayan zaman awanni takwas da gwamnatin tarayya ranar Juma'a, da yiwuwan kungiyar Likitoci NARD za ta janye yajin aikin a yau Asabar.

A cewar ThePunch, an samu labari daga ganawar da suka yi tun daga karfe 3 na rana zuwa 11 na dare ranar Juma'a cewa bangarorin biyu sun samu matsaya kuma sun rattafa hannayensu kan yarjejeniya.

Wata majiya ta ce Likitocin sun amince zasu janye yajin aikin da aka kwashe kwanaki tara yanzu anayi idan shugabannin kungiyarsu suka amince.

Wakilan Likitocin sun yi alkawarin ganawa da mambobinsu ranar Asabar, sannan su yanke shawara.

"An samu matsaya a ganawar kuma Likitocin sun amince da abubuwan da akayi na amsa bukatunsu. Saboda haka za su gana da mambobinsu ranar Asabar kuma su yanke shawara kan yajin aikin," majiyar tace.

KU KARANTA: Mun umurci Makiyaya suyi kaura daga jihar Ebonyi, Kungiyar Miyetti Allah

An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau
An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

Da farko, Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi iyakan kokarinta wajen amsa bukatun Likitocin guda bakwa.

Hakazalika kwamitin kiwon lafiya na majalisar wakilai ta zanna da Likitocin don rokonsu su janye yajin aiki don rayuwar talakawan dake kwance a asibitocin gwamnatin kuma ba za su iya zuwa na kudi ba.

Shugaban kwamitin, Tanko Sununu, yayin hira da manema labarai bayan zaman ya ce Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, zai gana da Likitocin ranar Talata.

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD da wasa da rayukan al'umma a wannan halin da kasa take ciki na tsanani.

Dr Chris Ngige, wanda shine ministan ayyuka da kwadago, ya jefa wannan zargin garesu ne a ranar Juma'a da suka shiga taro da likitocin a Abuja, babban birnin tarayya.

Ya ja kunnen 'yan kungiyar inda ya jefa wannan zargin a garesu inda yace suna kokarin fifita jindadi da walwalarsu sama da rayukan al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel