Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

- Wata mata yar Najeriya da ta zana hoton Ahmed Bola Tinubu a jikinta ta ce mijinta ya fitittiketa daga gida

- Matar mai suna @AyokunmiBabato1 a Tuwita ta yi kira ga yan Najeriya su kawo mata dauki

- A cewarta, ba tada wajen zuwa kuma dukkan yan'uwanta sun kaurace mata saboda abinda ta aikata

Matar da ta zana hoton babban jigon jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Tinubu a gadon bayanta ta kai kuka kafafen ra'ayi da sada zumunta bayan mijinta ya koreta daga gida.

Matar ta ce bayan da mijinta ya fitittiketa, yan'uwanta sun ce ba zasu yarda ta dawo gidansu ba.

Saboda haka ta garzaya shafinta na Tuwita don kira ga mutane su taimaketa, ba tada wajen kwana.

Matar mai suna @AyokunmiBabato1 a Tuwita tace:

"Mijina ya fitittikeni daga gida saboda zanen da nayi kuma ba ni da wajen zuwa. Ku taimakeni."

KU DUBA: Mun umurci Makiyaya suyi kaura daga jihar Ebonyi, Kungiyar Miyetti Allah

KU DUBA: An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

Miji na ya sake ni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka
Miji na ya sake ni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka
Asali: Twitter

A wani labarin kuwa, Masoya da magoya-bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, sun kaddamar da wani sabon ofishin kungiyar SWAGA 23 a jihar Ondo.

Kungiyar SWAGA 23 watau South West Agenda for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta na yi wa Bola Tinubu yakin neman zaben shugaban kasar Najeriya.

Da ake bude ofishin SWAGA 23 a Ondo, shugaban wannan tafiya, Sanata Dayo Adeyeye, ya ce kungiyar za ta ratsa duka kananan hukumomi 18 na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel