Yajin aiki: FG na zargin likitoci da wasa da rayukan 'yan Najeriya

Yajin aiki: FG na zargin likitoci da wasa da rayukan 'yan Najeriya

- Gwamnatin tarayya tana zargin kungiyar likitoci masu neman kwarewa da wasa da rayukan 'yan Najeriya

- Ministan kwadago da ayyuka, Dr Chris Ngige ne ya zargesu da hakan a ranar Juma'a a taron da suka yi da likitocin a Abuja

- Ya ja kunnensu da suyi gaggawar dakatawa da wasa da rayukan al'umma yayin da suke kokarin nema wa kawunansu walwala

Gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD da wasa da rayukan al'umma a wannan halin da kasa take ciki na tsanani.

Dr Chris Ngige, wanda shine ministan ayyuka da kwadago, ya jefa wannan zargin garesu ne a ranar Juma'a da suka shiga taro da likitocin a Abuja, babban birnin tarayya.

Ya ja kunnen 'yan kungiyar inda ya jefa wannan zargin a garesu inda yace suna kokarin fifita jindadi da walwalarsu sama da rayukan al'umma.

KU KARANTA: Jiya ba yau ba: Tsoffin hotunan biloniyoyi Dangote, Adenuga da Otedola sun bada mamaki

Yajin aiki: FG na zargin likitoci da wasa da rayukan 'yan Najeriya
Yajin aiki: FG na zargin likitoci da wasa da rayukan 'yan Najeriya. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A cewarsa NARD ko kuma NMA kungiyace ta kasuwanci kuma 'yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu sakamakon wannan yajin aikin.

A cewarsa yayin da 'yan kungiyar suke tunanin suna da hakki, ya kamata su gane matsalolin da suke jefa al'umma a ciki.

"Najeriya tana fuskantar matsalar annobar COVID-19 a halin da ake ciki. Ya kamata a samu sadaukarwa.

"Duk da hakan, wannan gwamnatin tana iyakar kokarinta wurin ganin ta karawa ma'aikatan lafiya walwala, wadanda suke yanzu aka fi bukata don yaki da wannan annoba," a cewar Ngige.

Ya kuma tunatar dasu rantsuwar da suka yi ta yin iyakar kokarinsu wurin ceto ran jama'a.

Karamin ministan lafiya, Dr Olorunnimbe Mamora, wanda yake cikin taron, ya roki likitoci da su yi gaggawar kawo karshen yajin aikin.

KU KARANTA: Aisha ta bayyana dalilinta na kalubalantar gwamnatin Buhari a wasu lokuta

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace ba zai baiwa wani mai garkuwa da mutane ko sisi ba koda kuwa dansa ne yake hannunsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirar gidan rediyo da aka yi dashi ranar Juma'a akan yadda gwamnatinsa take bullo wa 'yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya dade yana bayyana yadda yake amfani da karfi wurin magance ta'addanci a jiharsa, kuma yana tsaye akan bakarsa. Ya maimaita a ranar Alhamis cewa babu wani dan ta'adda daya dace ya rayu a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel