Ina dan hutawa ne a Landan, Shugaba Buhari ya yi magana daga Birtaniya

Ina dan hutawa ne a Landan, Shugaba Buhari ya yi magana daga Birtaniya

- Makon shugaba Buhari daya yanzu a birnin Landan

- Sabanin abinda hadimansa suka fada na cewa ya tafi jinya, Buhari ya ce hutawa ya tafi yi

- Hakan ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana dan hutawa ne a Landan, kasar Birtaniya.

Buhari ya bayyana hakan ne a wasika ta musamman da ya aike ga Sarkin Urdu, Abdullah ll Bin Al-Hussein, kan rikicin da masarautarsa tayi fama da shi kwanakin baya.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki mai taken: "Shugaba Buhari ya aike wasika ga Sarkin Urdu Abdullah, yana masa fatan Alheri."

A cewar Garba Shehu, Buhari ya yi matukar damuwa lokacin da ya samu labarin abubuwan da ke faruwa a masarautar kadar amma ya ji dadin samun labarin cewa komai ya yi daidai yanzu.

KU KARANTA: Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

Ina dan hutawa ne a Landan, Shugaba Buhari ya yi jawabi daga Birtaniya
Ina dan hutawa ne a Landan, Shugaba Buhari ya yi jawabi daga Birtaniya Credit: Presidency

DUBA NAN: Dangote bai son ganin kowa yayi takara a kasuwanci da shi, AbdulSamad Rabiu BUA

Ya ruwaito Buhari da cewa: "Yayinda nike Landan ina dan hutawa, na yi matukar damuwa kan labarin da na samu cewa wasu na kokarin tayar da tarzoma a masarautar Urdu."

"Amma mutuncinka da iya shugabancinka ya janyo hankalin kasashen duniya gaba daya."

"Mai martaba, ina farin ciki an sassauta abubuwa yanzu kuma ina addu'a masarautar Hashimiya za ta cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya da lumana."

A bangare guda, Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, tayi bayani cikin sabon littafinta dalilinta da yasa ta zabi yin jinya a Najeriya maimakon zuwa Landan lokacin da tayi rashin lafiya.

A Littafin mai suna: 'Aisha Buhari: Ta daban ce', uwargidar shugaban kasan ta bayyana halin da asibitin fadar shugaban kasa yake a lokacin.

Hajo Sani, babbar hadimar shugaban kasa kan harkokin mata ce ta rubuta littafin, wanda ya hada da tarihin Aisha Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel