Dangote bai son ganin kowa yayi takara a kasuwanci da shi, AbdulSamad Rabiu BUA

Dangote bai son ganin kowa yayi takara a kasuwanci da shi, AbdulSamad Rabiu BUA

- Ana musayar zargi tsakanin manyan attajiran Najeriya biyu

- Aliko Dangote da AbdulSamad Isyaka Rabiu na cikin jerin mutane mafi arziki a Najeriya

- Isyaka Rabiu na zargin Dangote da yi masa zagon kasa ta hanyar kai kararsa wajen hukuma

Kamfanin BUA ya mayar da martani kan ikirarin kamfanin Dangote da kamfanin Flour Mill cewa matatar sukarin BUA dake garin Fatakwal matsala ce ga kamfanonin sukari a Najeriya, rahoton TheCable.

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da shugaban Flour Mill, John Coumantaros, sun aike wasika ga Ministan kasuwanci da masana'antu inda suka tuhumi matatar sukarin BUA na saba tsarin sukari na Najeriya (NSMP).

Tsarin NSMP wani shiri ne da aka yi a 2013 na tabbatar da cewa Najeriya ta samu isasshen sukari da zai isa al'umma.

DUBA NAN: Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gini da robobin ruwa a Kaduna

Dangote bai son ganin kowa yayi takara a kasuwanci da shi, AbdulSamad Rabiu BUA
Dangote bai son ganin kowa yayi takara a kasuwanci da shi, AbdulSamad Rabiu BUA Credit: BUA/Dangote
Asali: Twitter

DUBA NAN: Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

Martani kan hakan, shugaban BUA AbdulSamad Rabiu ya ce matatar sukarinsa na bin ka'idar NEPZA da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Isyaka Rabiu ya ce Dangote da Coumantaros na kokarin "fito-na-fito da umurnin shugaban kasa da kuma mutuncin ma'aikatar kasuwanci da masana'antu."

"Saboda haka muna ganin wannan fito-na-fito ne ga ikon shugaban kasa da kuma yunkurin raina hankalin Najeriya da ma'aikatunta da kuma kokarin dakile abokan takara, don su zama su kadai ke kasuwancin sukari kuma kasar ta wahala," yace.

Kowa ya san cewa "a Najeriya da duniya, duk inda Dangote dake harka ko kasuwanci bai san ganin kowa a wajen kuma ya kan yi iyakan kokarinsa wajen dakile mutum" kuma "hakan yake sake yi yanzu." Ya kara.

Wasikar Dangote

A wasikar mai ranar wata, 8 ga Junairu 2021, Dangote da Coumantaros, sun aike wasika ga minista Niyi Adebayo, inda suka zargi matatar sukarin dake Fatakwal da cewa an ginata ne domin sabawa tsarin NSMP.

Sun bukaci Ministan ya binciki adadin danyen sukarin da BUA ke kawowa Najeriya kuma ya ci su tarar da ya kamata.

A bangare guda, shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya aiki ba muddin ba'a biyan kudin haraji da kuma sayan man fetur a farashin da ya kamata.

Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, rahoton The Punch.

Kwamitin zaman lafiyan kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdus Salam Abubakar (Mai ritaya) ce ta shirya taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel