Da nayi rashin lafiya, a Najeriya na yi jinya ban tafi Landan ba: Aisha Buhari

Da nayi rashin lafiya, a Najeriya na yi jinya ban tafi Landan ba: Aisha Buhari

- Tinubu, Osinbajo, Sarkin Musulmi sun halarci taron kaddamar da littafin Aisha Buhari

- Daya daga cikin hadiman Buhari ce ta rubuta littafin don karramar uwar gidan shugaban kasan

- Aisha ta bayyana rashin lafiyan da tayi amma ta gaza yin jinya a fadar shugaban kasa

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, tayi bayani cikin sabon littafinta dalilinta da yasa ta zabi yin jinya a Najeriya maimakon zuwa Landan lokacin da tayi rashin lafiya.

A Littafin mai suna: 'Aisha Buhari: Ta daban ce', uwargidar shugaban kasan ta bayyana halin da asibitin fadar shugaban kasa yake a lokacin.

Hajo Sani, babbar hadimar shugaban kasa kan harkokin mata ce ta rubuta littafin, wanda ya hada da tarihin Aisha Buhari.

DUBA NAN: Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gini da robobin ruwa a Kaduna

Da nayi rashin lafiya, a Najeriya na yi jinya ban tafi Landan ba: Aisha Buhari
Da nayi rashin lafiya, a Najeriya na yi jinya ban tafi Landan ba: Aisha Buhari Credit: Presidency

KU KARANTA: Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

Wani sashen littafin yace: "Wani abu da ta tayar da kura shine jawabinta na ranar 9 ga Oktoba ...inda tayi magana kan muhimmancin kiwon lafiya. Ta yi alhinin yadda ake bata shawaran tafiya Landan lokacin da tayi rashin lafiya, amma ta ki."

"Abin takaici, asibitin fadar shugaban kasa na da matsaloli kuma babu kayan aikin da zai iya kula da lafiyan iyalin shugaban kasa da manyan jami'an gwamnati."

"A lokacin ne ta caccaki shugabannin asibiti saboda babu kayayyakin kula da lafiya a asibitin. A cewarta, sai da ta tafi wani asibiti mai zaman kansa tayi jinya."

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana dan hutawa ne a Landan, kasar Birtaniya.

Buhari ya bayyana hakan ne a wasika ta musamman da ya aike ga Sarkin Urdu, Abdullah ll Bin Al-Hussein, kan rikicin da masarautarsa tayi fama da shi kwanakin baya.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki mai taken: "Shugaba Buhari ya aike wasika ga Sarkin Urdu Abdullah, yana masa fatan Alheri."

Asali: Legit.ng

Online view pixel