Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

- Dangote ya tofa albarkacin bakinsa kan magance matsalar tsaro a Najeriya

- Attajirin ya bayyana cewa babu yadda za'ayi gwamnati ta samu kudi idan ba'a biyan kudin haraji

- Hakazalika a bayyana bukatar sanya farashin mai da ya kamata sabanin yadda ake yanzu

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya aiki ba muddin ba'a biyan kudin haraji da kuma sayan man fetur a farashin da ya kamata.

Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, rahoton The Punch.

Kwamitin zaman lafiyan kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdus Salam Abubakar (Mai ritaya) ce ta shirya taron.

Dangote yace, "Ta yaya gwamnati za tayi aiki ba'a biyanta kudin haraji. Ya kamata a biya haraji; idan aka ce za'a kara, mutane sai su fara kuka. Ana son a sanya farashin mai da ya kamata amma wasu zasu ce sam kada a yi."

"Ta ina za'a samu kudi toh? Saboda haka wannan aikin kowa ne. Idan kuna son tsaro, wajibi ne ku bada naku gudunmuwar. Ba kyauta za'a baku tsaro ba."

KU DUBA: Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gini da robobin ruwa a Kaduna

Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote
Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

KU KARANTA: Ina dan hutawa ne a Landan, Shugaba Buhari ya yi magana daga Birtaniya

Dangote ya kara da cewa lamarin tsaro matsalar kowa ne. Saboda ko yan kasuwa ba zasu iya kasuwancinsu yadda ya kamata ba idan babu tsaro.

A cewarsa, "wannan shine dalilin da ya sa yan kasuwa masu zaman kansu suka yi alkawarin bada gudunmuwar N100bn don taimakawa yan sanda."

A bangare guda, kamfanin BUA ya mayar da martani kan ikirarin kamfanin Dangote da kamfanin Flour Mill cewa matatar sukarin BUA dake garin Fatakwal matsala ce ga kamfanonin sukari a Najeriya.

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da shugaban Flour Mill, John Coumantaros, sun aike wasika ga Ministan kasuwanci da masana'antu inda suka tuhumi matatar sukarin BUA na saba tsarin sukari na Najeriya (NSMP).

Tsarin NSMP wani shiri ne da aka yi a 2013 na tabbatar da cewa Najeriya ta samu isasshen sukari da zai isa al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel