Da duminsa: An gano abu da ake zargin Bam ne a cikin makarantar firamare a jihar Abiya
- Abubuwa sun juya kan matsalar tsaro a Najeriya yayinda hankali ya koma yankin kudu maso yamma
- Bayan harin da ake kaiwa ofishohin yan sanda, yan bindiga sun kubutar da fursunoni akalla 2000
- Yanzu kuma an gano Bam cikin makarantar firamare a yankin
An tsinci wani abin fashewa da ake zargin Bam ne a makarantar firamaren Afara Unity School dake karamar hukumar Umuahia North a jihar Abiya ranar Alhamis.
An umurci dukkan daliban makarantar su koma gida har sai an tabbatar da babu abin da zai cutar da su.
Jami'an dakile Bam na hukumar yan sanda sun dira makarantar yanzu haka.
Gwamnatin jihar Abia ta bayyana cewa ita da hukumomin tsaro na tattaunawa kan lamarin.
Kwamishanan labaran jihar, Cif John Kalu, ya bayyanawa manema labarai cewa abin da suka gani na da alamun abubuwan da akayi amfani dasu lokacin yakin basasa, rahoton Daily Trust.
Ya kara da cewa ana sauraron rahoton binciken da jami'an yan sanda ke gudanarwa.
KU DUBA: Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote

Asali: Original
DUBA NAN: Ina dan hutawa ne a Landan, Shugaba Buhari ya yi magana daga Birtaniya
A bangare guda, ana cigaba da zaman dar-dar a jihar Imo a yayin da yan bindiga a safiyar ranar Alhamis suka kai hari hedkwatan 'yan sanda da ke Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli, The Punch ta ruwaito.
Wani mazaunin Mbieri ya shaida masa cewa yan bindigan sun kai hari misalin karfe daya na daren nan take suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.
Ya ce yan bindigan sun kuma sace wayoyin salula mallakar wadanda ake tsare da su da na yan sandan da ke ofishin.
Asali: Legit.ng