Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun sake kai hari ofishin ƴan sanda a Imo, sun sace guda, sun raunta wasu

Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun sake kai hari ofishin ƴan sanda a Imo, sun sace guda, sun raunta wasu

- 'Yan bindiga sun sake kai hari a wani ofishin 'yan sanda da ke Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli jihar Imo

- Bayan fafatawa da yan sandan, yan bindigan sun yi nasarar sace guda sun kuma saki wadanda ake tsare da su

- Orlando Ikeokwu, kakakin rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da kai harin inda ya ce an fara bincike nan take

Ana cigaba da zaman dar-dar a jihar Imo a yayin da yan bindiga a safiyar ranar Alhamis suka kai hari hedkwatan 'yan sanda da ke Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli, The Punch ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ce wani mazaunin Mbieri ya shaida masa cewa yan bindigan sun kai hari misalin karfe daya na daren nan take suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake kai hari ofishin 'yan sanda a Imo, sun sace jami'i daya, sun raunta wasu
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake kai hari ofishin 'yan sanda a Imo, sun sace jami'i daya, sun raunta wasu
Asali: Original

Ya ce yan bindigan sun kuma sace wayoyin salula mallakar wadanda ake tsare da su da na yan sandan da ke ofishin.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Amma majiya daga ofishin yan sanda ta shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa yan sandan da ke kan aiki sun dakile harin da yan bindigan suka yi niyyar kai wa.

Dan sandan ya ce, "Mun fafata da su amma sun fi karfin mu. Makamansu sun fi namu. Sun sace dukkan wayoyin da suka gani a nan, sannan sun saki dukkan wadanda ake tsare da su sun lalata ginin ofishin mu."

Majiyar ya ce maharan sun sace dan sanda daya sun kuma raunta wasu jami'n.

Kakakin yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da harin da aka kai ofishin na yan sandan a yayin da ake tuntube shi a safiyar ranar Alhamis.

KU KARANTA: Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

Ya kuma tabbatar da cewa ba a ga dan sanda daya ba sannan biyu sun jikkata sakamakon artabun da suka yi da yan bindigan.

Ikeokwu ya kuma tabbatar da cewa maharan sun saki wadanda ake tsare da su a caji ofis din.

Ya kuma bada tabbacin cewa rundunar ta fara bincike kan harin nan take.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: