Ta tabbata: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai

Ta tabbata: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai

- Akalla mutum 18 sun rasa rayukansu bayan yin rigakafin cutar Korona

- Bayan watanni ana cece-kuce, an tabbatar da rigakafin na haddasa daskarewar jini

- Yayinda wasu suka samu daskarewa a kwakwalwa, wasu a cikin tumbi suka samu

Hukumomi a Turai sun tabbatar da cewa akwai alaka tsakanin daskarewar jini da rigakafin Koronan Oxford-AstraZeneca.

Hakazalika hukumomi a kasar Birtaniya sun bada shawaran cewa matasa yan shekara kasa da 30 kada su yi rigakafin.

A cewar rahoton CNN, hukumar bibiyar magungunan ta Turai European Medicines Agency (EMA) a ranar Laraba ta ce a lissafa daskarewar jini cikin matsalolin rigakafin kuma a rage amfani da shi.

Duk da haka, hukumar EMA ta bayyana cewa amfanin rigakafin ya rinjayi matsalar saboda COVID-19 muguwar cuta ce.

DUBA NAN: Ba ceto mu Soji sukayi ba, yan bindigan suka sakemu da kansu: Daliban Kaduna sun karyata hukuma

Ta tabbata: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai
Ta tabbata: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai
Asali: Twitter

KU KARANTA: Muggan makamai Sama da miliyan 6 ke shawagi a faɗin ƙasar nan, Inji Janar Abdussalami

Su kuma hukumomi a kasar Birtaniya sun bada shawarar cewa masu shekaru kasa da 30 su nemi wani rigakafin sabanin Oxford-Astrazeneca.

Za ku tuna cewa irin wannan rigakafin aka kawo wa Najeriya karkashin shirin COVAX.

Manyan jami'an gwamnati da jama'a sun yi rigakafin a Najeriya.

Jami'an EMA sun bayyana cewa sun yi bincike kan labarin mutuwar mutum 18.

Mutanen na cikin jerin 62 da aka samu da daskarewar jini a kwakwalwa da hanci, yayinda 24 suka samu daskarewa a tumbi bayan musu rigakafin Oxford-Astrazeneca.

A bangare guda, aƙalla 79 sun kamu da cutar daskarewar jini a Burtaniya bayan anyi musu allurar rigakafin Astrazeneca.

Shugaban hukumar ƙayyade magunguna na Burtaniya (MHRA), June Raine, shine ya faɗi haka a wani taro da suka yi.

Shugaban MHRA ya bayyana cewa daga sanda ƙasar ta ƙaddamar da fara yin allurar rigakafin zuwa 31 ga watan Maris ɗin da ya gabata, an yiwa mutane 20 miliyan a karon farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel