Ba ceto mu Soji sukayi ba, yan bindigan suka sakemu da kansu: Daliban Kaduna sun karyata hukuma

Ba ceto mu Soji sukayi ba, yan bindigan suka sakemu da kansu: Daliban Kaduna sun karyata hukuma

- Dalibai biyar cikin 39 da aka sace a makaranta a Kaduna sun samu kubuta

- Hukumar Sojin Najeriya ta saki sunayensu ranar Laraba

- An shiga rudani yayinda aka samu tanakudi kan yadda daliban suka kubuta

Daya daga cikin daliban makarantar FCFM dake Afaka, jihar Kaduna ya yi bayani kan ainihin yadda suka samu kubuta daga hannun yan bindiga.

Mun kawo muku cewa Hukumar Sojin Najeriya ta saki sunayen daliban makarantar FCFM Afaka, jihar Kaduna da aka ceto bayan garkuwa da su a harin da aka kai makarantar ranar 11 ga Maris, 2021.

A cewar Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Mohammed Yerima, an samu nasarar ceto biyar cikin dalibai 39 da aka sace.

Daliban Abubakar Yakubu, Francis Paul, Obadiya Habakkuk, Amina Yusuf da Maryam Danladi, a cewarsa.

Amma a hirar da Daily Trust tayi da daya daga cikin daliban, Francis Paul, ya bayyana cewa yan bindigan ne suka sakesu da kansu.

"Wata rana suka zo suna zaban wasu daga cikinsu....lokacin ma ina rashin lafiya. Sai suka ce in zauna a gefe guda, sannan suka zabi wasu yan mata suka dauramu kan babur. Sai suka ajiyemu a wani kauye kusa da kan hanya kuma suka ce mu tafi," yace.

KU KARANTA: Kwamishinan Yan sandan Lagos ya ɗauki ƙwaƙkwaran Mataki don gujema abinda ya faru a Owerri

Karya ne ba ceto mu Soji sukayi ba, yan bindigan suka sakemu da kansu: Daliban Kaduna
Karya ne ba ceto mu Soji sukayi ba, yan bindigan suka sakemu da kansu: Daliban Kaduna
Source: Twitter

KU KARANTA: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai

A wani labarin kuwa, hawaye sun kwaranya a sakatariyar karamar hukumar Jema'a dake Kafanchan, jihar Kaduna ranar Laraba yayinda gwamnatin jihar ta mika wasikun sallama ga wasu ma'aikata 82.

Wannan sabon kora ya biyo bayan jita-jitan da aka kwashe makonni ana ji cewa gwamnatin jihar na shirin rage ma'aikata a kananan hukumomin 23.

Yayinda kamfanin dillancin labarai NAN ta ziyarci Sakatariyar, an ga ma'aikatan rike da takardunsu cikin takaici da bakin ciki.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel