Mutane 79 sun kamu da daskarewar Jini bayan musu rigakafin Astrazeneca, 19 cikinsu sun mutu

Mutane 79 sun kamu da daskarewar Jini bayan musu rigakafin Astrazeneca, 19 cikinsu sun mutu

- A wani rahoto da ƙasar Burtaniya ta fitar ya nuna cewa kimanin mutum 79 sun kamu da cutar daskarewar jini bayan an musu rigakafin Astrazeneca a karon farko

- Shugaban hukumar MHRA ya ce daga lokacin da aka fara rigakafin zuwa ran 31 ga watan Maris an yiwa mutane 20 miliyan allurar rigakafin a karon farko

- Sai dai a Najeriya, hukumomi sun ce bayan sati ɗaya da fara yiwa yan ƙasa allurar rigakafin Astrazeneca, ba'a samu wata matsala ta daskarewar jini ba a faɗin ƙasar

Aƙalla 79 sun kamu da cutar daskarewar jini a Burtaniya bayan anyi musu allurar rigakafin Astrazeneca.

KARANTA ANAN: Kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmuwar rigakafin Korona guda 100,000

Shugaban hukumar hukumar ƙayyade magunguna na Burtaniya (MHRA), June Raine, shine ya faɗi haka a wani taro da suka yi.

Shugaban MHRA ya bayyana cewa daga sanda ƙasar ta ƙaddamar da fara yin allurar rigakafin zuwa 31 ga watan Maris ɗin da ya gabata, an yiwa mutane 20 miliyan a karon farko.

Ya kuma ƙara da cewa, a wannan lokacin an samu waɗanda suka kamu da cutar daskarewar jini bayan an musu rigakafin su 79.

Mutane 79 sun kamu da cutar daskarewar Jini bayan musu rigakafin Astrazeneca, 19 daga cikinsu sun mutu
Mutane 79 sun kamu da cutar daskarewar Jini bayan musu rigakafin Astrazeneca, 19 daga cikinsu sun mutu Hoto: @Channelstv
Source: Twitter

Daga cikin mutane 79 da suka kamu da daskarewar jinin, 19 daga cikin run riga mu gidan gaskiya.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Osinbajo ya rantsar da sabon Sifetan Yan Sanda, Alkali

A satin nan ne dai kwamitin yaƙi da cutar COVID19 ta ƙasar mu Najeriya ya bayyana cewa bayan mako ɗaya da fara rigakafin cutar ta Astrazeneca, ba'a samu wanda ya kamu da daskarewar jini ba.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa ya zuwa yanzun an yiwa yan Najeiya 964,387 rigakafin ta Astrazeneca.

Ya ce gwamnatin tarayya na son a cikin shekaru biyu masu zuwa, ta yi wa yan Najeriya 70% rigakafin kafin ƙarewar shekarar 2022.

A wani labarin kuma Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya zabi Ahmed Garba matsayin Sabon sarkin Kagara

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya amince da naɗin Ahmed Garba Gunna a matsayin sabon sarkin Kagara

An naɗa sabon sarkin ne biyo bayan rasuwar sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko, wanda ya rasu ranar 2 ga watan Maris ɗin da ya gabata.

Source: Legit

Online view pixel