Muggan makamai Sama da miliyan 6 ke shawagi a faɗin ƙasar nan, Inji Janar Abdussalami

Muggan makamai Sama da miliyan 6 ke shawagi a faɗin ƙasar nan, Inji Janar Abdussalami

- Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, janar Abdussalami Abubakar ya ce akwai kimanin muggana makamai miliyan N6m dake yawo a Najeriya ba bisa ƙa'ida ba

- Tsohon shugaban wanda shine shugaban kwamitin zaman lafiya ya bayyana haka ne yau Laraba bayan wani taro a Abuja

- Ya ce jami'an tsaron mu na buƙatar makamantan makaman ko wanda suka fisu da kuma samun isassun kuɗaɗe domin shawo kan matsalar tsaro

Tsohon shugaban Najeria a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ya gargaɗi yan Najeriya kan yawaitar muggan makamai dake yawo a kasar nan.

Ya ce akwai muggan makamai dake shawagi a cikin Najeriya sama da miliyan N6m ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: A yayinda ake tsaka da annobar COVID-19, FG ta tabbatar da yaduwar wata mummunar cuta a Jihohi 7

Abdussalami Abubakar, wanda shine shugaban kwamitin zaman lafiya (NPC) ya yi wannan gargaɗi ne a wani taro da suka yi da masu ruwa da tsaki a Abuja yau Laraba.

Abdussalami ya ce, yawaitar makaman a ƙasa shine yake jawo ƙaruwar matsalolin tsaro da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 80,000.

Ya ce ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta bawai rashin tsaro ne kaɗai ba, akwai wasu matsalolin na rayuwa.

Matsalar Tsaro: Muggan makamai Sama da miliyan N6m ke shawagi a faɗin ƙasar nan, inji janar Abdussalami
Matsalar Tsaro: Muggan makamai Sama da miliyan N6m ke shawagi a faɗin ƙasar nan, inji janar Abdussalami Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta kamar; Rikicin Boko Haram, fashi da makami, satar mutane domin neman kuɗin fansa, ƙaruwar talauci da tsadar rayuwa, kira ga rarraba ƙasa da wasu ke yi.

KARANTA ANAN: Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba

Ya ƙara da cewa akwai ƙalubalen yunwa da rashin tsaro ke jawo wa, wanda manoma ke fuskanta kuma suke cigaba da fuskanta, da dai sauran su.

Ya ce wata matsalar kuma itace yawaitar muggan makamai dake yawo, ba wai a wasu yankuna kaɗai ba, a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Ya kara da cewa a halin yanzun ana ƙiyasin akwai sama da makamai miliyan N6m dake yawo a faɗin ƙasar nan.

Wanda wannan shine yake ƙara yawaitar matsalolin tsaro, wanda ya jawo mutuwar mutane sama da 80,000 da kuma fitar da mutane kusan miliyan N3m daga mahallinsu.

Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce jami'an tsaron mu zasu yi matuƙar ƙoƙari wajen shawo kan matsalar idan aka samar musu da makaman da yakamata da kuɗaɗe yadda yakamata.

A wani labarin kuma Gurgu ya hargitsa gangamin APC, ya yi wa Shugaban karamar hukuma ihun ‘Ba mu so’

Wani bidiyo ya zagaye kafofin yada labarai inda aka ga wani Bawan Allah ya na yi wa shugabannin jam’iyyar APC ihun bore da rana-tsaka.

Wani wanda ake kira Kwankwason Twitter shi ne ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel