Yanzu-Yanzu: An ɗage rubuta jarrabawar WASSCE ta 2021 saboda annobar korona

Yanzu-Yanzu: An ɗage rubuta jarrabawar WASSCE ta 2021 saboda annobar korona

- Hukumar jarrabawar WAEC ta ce ba za a rubuta jarrabawar bana a watan Mayu da Yuni ba

- Mr Patrick Areghan, shugaban hukumar a Nigeria, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Legas

- Mr Areghan ya ce annobar korona ce ta hargista jadawalin jarrabawar na 2021 don haka za a fitar da wani jadawalin a nan gaba

An dage fara rubuta jarrabawar Kammala Sakandare, WASSCE, har zuwa wani lokaci a nan gaba saboda radadin annobar korona, Vanguard ta ruwaito.

Da ya ke yi wa manema labarai a ranar Talata a Legas yayin sanarwar fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na Private ta shekarar 2021, shugaban hukumar, Mr Patrick Areghan ya yi bayanin cewa annobar korona ya hargitsa tsarin rubuta jarrabawar don haka ba zai yi wu a rubuta a watan Mayu da Yuni ba.

Yanzu-Yanzu: An ɗage rubuta jarrabawar WASSCE ta 2021 saboda annobar korona
Yanzu-Yanzu: An ɗage rubuta jarrabawar WASSCE ta 2021 saboda annobar korona. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Ya ce: "Ina son yin amfani da wannan damar domin karin haske kan jita-jitar da ake yadawa kan jarrabawar WASSCE ta dalibai na 2021. Har yanzu ana jin radadin annobar korona a bangaren ilimi.

"Jadawalin jarrabawar ya hargitse, don haka ba zai yi wu a rubuta jarrabawar a watannin Mayu da Yuni a bana ba. Za a fitar da sabon jadawalin a nan gaba."

Dukkan masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri su saurari sanarwa daga WAEC.

KU KARANTA: Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina

Shugaban na WAEC ya kuma roki shugabannin makarantu su yi wa dalibansu rajista a kan lokaci.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel