Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina

Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina

- Injiniya Kabir, wani mazaunin Katsina ya bawa kayatar da mutane saboda basirarsa na hada babura

- Hotunan baburan da aka ce Kabiru ya kera sun bazu a shafukan dandalin sada zumunta inda yake ta shan yabo

- Wasu sun yi kira ga gwamnatin ta tallafa masa ya inganta aikinsa ya kuma samu damar hada su da yawa

Wani dan Nigeria da aka ce sunansa Injiniya Kabir ya burge yan Nigeria da baiwa da Allah ya bashi na hada babura.

Wani sako da Gen. Yunus Jnr, @yunusxonline, ya wallafa a Twitter ya bayyana cewa Injiniya Kabir wanda ke Garejin Ali Chizo ba yi karatun makarantar Boko Ba.

Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina
Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina. Abdullahi Bambale
Asali: Facebook

A gano wani sako mai kama da wannan a shafin wani Abdullahi Bambale a Facebook inda ya wallafa lambobin wayoyin Injiniya Kabir (07063146240 da 08155894355) ga duk wani mai son siyan abubuwan da ya ke kerawa ko neman ya yi masa wani aikin.

KU KARANTA: Yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta laƙume gidansu a Suleja

Yan Nigeria da dama sun nuna gamsuwarsu da sha'awa bisa basirar da Kabir ke da shi inda suka rika yaba masa.

Babatunde Matanmi ya ce a Facebook.

"Wannan abin ya yi kyau sosai, sannu da aiki. Ina ganin ya kamata ya saka masu suna Kabircycle."

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna

Taiwo Modupe Awosika ya ce:

"Wata kamfani a Nigeria na iya sarrafa wannan baburan da yawa. Idan wannan abin ya kai China, za su sarrafa su da yawa su sayar mana. Wannan ya yi kyau sosai."

Adebiyi Mayowa Angelmayor ya ce:

"Abin dariya Kungiyar Injiniyoyi ta Nigeria na iya cewa kada a kira wannan mutumin Injiniya saboda ba shi da takardun makaranta da suka tafi suka samo a kwallejin fasaha ko jami'a ba tare da samun fasaha ta azo-a-gani ba."

Akinlolu Akinnifesi ya ce:

"Lallai! Allah ya yi wa hannunsa Albarka."

Shafbeyioku, @shafbeyioku, a Twitter ya ce:

"Da gaske? Gwamnatin Tarayya ta samu masu kera ababen hawa su yi hadin gwiwa da wannan mutumin ba tare da an cuce shi ba."

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel