Saƙon Easter: Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana abin da yasa jawabin Kukah ba ta yi kama da na malamin addini ba

Saƙon Easter: Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana abin da yasa jawabin Kukah ba ta yi kama da na malamin addini ba

- Fadar Shugaban kasa ta soki kalaman Kukah tare da bayyana cewa akwai son zuciya a ciki

- Garba Shehu, ya ce bai kamata malamin addini ya nuna bangaranci ba yayin fadar gaskiya

- Fadar ta bukaci yan kasa su ci gaba da goyawa gwamnatin Buhari baya don ciyar da kasa gaba

Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Saƙon Easter: Kukah bai yi magana irin ta malaman addini ba, Fadar Shugaban Ƙasa
Saƙon Easter: Kukah bai yi magana irin ta malaman addini ba, Fadar Shugaban Ƙasa. Hotuna: Femi Adesina/Facebook. @Mr_JAGs/Twitter
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Ya ce malamin ya jefa siyasa a wasu jawabai da ya yi a sakon bikin ranar Easter.

Sanarwar ta ce, "kowane dan kasa yana da ra'ayin sa, kowa ma da kalar yardar sa.

"Amma idan kace kai malamin addini ne, kamar yadda dattijo Mathew Hassan Kukah yayi, bai kamata bangaranci ya shiga ciki wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

"Dattijo Kukah ya fadi wasu abubuwa masu ma'ana a sakon sa na Easter.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

"Amma, fadin sa cewa ta'addancin Boko Haram yafi kamari fiye da 2015, bai dace ba a matsayin sa na malami. Kukah yaje Borno ko Adamawa ya tambayi mutanen yankin bambancin 2014 da kuma 2021.

"Bugu da kari, batun Hijab a Jihar Kwara wanda ya zayyano batu ne wanda kotun jihar tayi watsi da shi. Batutuwa ne da suka bulla jihohi da dama lokacin mulkin Obasanjo. A duk wannan yaushe kuma a ina sunan Buhari ya fito?

Yana saka siyasa ta hanyar janyo shugaban kasa cikin batun.

"Gwamnatin da ta kirkiri ma'aikata guda, a karon farko a tarihin kasar, tare da samar da wadatattun kayan aiki, don magance matsalar nakasassu, ba za a taba cewa ta kowacce hanya bata nuna musu kula ba.

"Wasu daga cikin kalaman na Kukah son zuciya ne kawai don cimma wata manufa.

"Muna kira ga yan kasa na gari da su cigaba da goyawa gwamnatin Buhari baya don tsare kasar tare da ciyar da ita gaba."

A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel