'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

- Yan sanda sun yi nasarar kashe wani hatsabibin shugaban yan bindiga a jihar Zamfara

- Sanawar da rundunar ta fitar ya ce jami'an Puff Adder II ne suka kashe shi a kauyen Tsibiri kusa da dajin Sububu

- Yan sandan sun kuma yi artabu da wasu yan bindigan inda suka kashe guda suka kwato makamai da layyu

'Yan sanda a jihar Zamfara sun halaka wani kasurgumin shugaban yan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo saboda adabar mutanen garuruwa daban-daban a jihar.

Jami'an yan sandan Operation Puff Adder II ne suka kashe hatsabibin dan bindigan yayin sintiri a kauyen Tsibiri kusa da dajin Sububu a karamar hukumar Maradun na jihar, TVC ta ruwaito.

'Yan sanda sun kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga a Zamfara
'Yan sanda sun kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga a Zamfara. Hoto: @TVCNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

Yan sandan sun kuma damke wasu yan bindiga da ake zargin suna hanyarsu ne na kai hari a wani gari da ke kusa da dajin.

Sanarwar da rundunar yan sandan ta fitar ya ce yan sandan sun yi musayar wuta da miyagun inda suka kashe daya yayin da saura suka tsere cikin dajin da raunukan bindga.

Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindiga AK-47, harsashi, babur da wata jaka dauke da layyu da kuma kayan sojoji.

KU KARANTA: Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

Yan sanda a jihar ta taba mutane tabbacin cewa za ta cigaba da yaki da dukkan yan bindigan da suka ki rungumar shirin sulhu da afuwa na gwamnatin jihar har sai an dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164