Atiku ya na fuskantar danyen kalubale game da zaben 2023 daga Gwamnatin Buhari

Atiku ya na fuskantar danyen kalubale game da zaben 2023 daga Gwamnatin Buhari

- AGF ya sanar da Kotu cewa Jagoran adawa, Atiku Abubakar ba ‘Dan Najeriya bane

- Ministan shari’ar ya ce Atiku Abubakar bai isa ya yi takarar Shugaban kasa ba

- Abubakar Malami ya ce a lokacin da aka haifi Atiku, Jada ba ta cikin Najeriya

Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce dokar kasa ba ta ba Atiku Abubakar damar neman shugaban kasa ba.

Malami ya hakikance a kan cewa ba mutanen Najeriya su ka haifi tsohon mataimakin shugaban kasa ba, don haka ba zai iya fito wa takara a zabe ba,

A cewar Ministan shari’an, idan aka bar Atiku Abubakar ya fito takara, an saba wa sasssa na 25(1), (2) da kuma sashe na 131(a) na dokar kasa dokar zabe na kasa.

The Nation ta ce Ministan ya kai wannan magana ne gaban babban kotun tarayya da ke garin Abuja.

KU KARANTA: Rabon jam’iyyar APC da kiran gangami tun 2020 - PGF

Abubakar Malami ya na da ja game da salsalar ‘dan siyasar, ya roki Alkali ya duba yadda aka haifi Atiku Abubakar, ya hana shi tsaya wa takarar shugaban Najeriya.

Tun kafin zaben 2019 ne Lauyoyin AGF a karkashin Oladipo Okpeseyi su ka shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, da har yau ba a saurara ba.

Rahotanni sun bayyana cewa za a zauna game da wannan shari’a a ranar 4 ga watan Mayu, 2021.

AFG ya kafe a kan cewa an haifi Atiku ne a shekarar 1946 a garin Jada, a wancan lokaci wannan yanki na Jada ya na cikin Arewacin Kamaru, kafin ya shigo Najeriya.

Atiku ya na fuskantar danyen kalubale game da zaben 2023 daga Gwamnatin Buhari
AGF Abubakar Malami
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun fake da ‘gobara’, su na neman jawo Matawalle

Sai a 1961 ne aka dawo da Jada cikin Najeriya, don haka Malami ya ce Atiku bai da hurumin da zai nemi kujerar shugaban kasa domin shi ba haifaffen Najeriya ba ne.

Ministan ya ce har iyayen tsohon mataimakin shugaban kasa su ka bar Duniya, su ba ‘yan Najeriya bane.

Kwanaki Adamu Atiku-Abubakar, ‘dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce mahaifinsa zai sake fitowa takarar shugaban kasa.

Alhaji Adamu Atiku-Abubakar wanda Kwamishina ne, ya bayyana wannan ne sa'ilin da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel