Sauya-sheka: Manyan Jiga-jigan Gwamnonin APC sun ziyarci Gwamnan jihar Zamfara

Sauya-sheka: Manyan Jiga-jigan Gwamnonin APC sun ziyarci Gwamnan jihar Zamfara

- Manyan Gwamnonin APC sun kai wa Bello Matawalle ziyara a Zamfara

- Gwamnonin sun yi amfani da damar gobarar da aka yi ne, sun tallata APC

- Akwai yiwuwar Gwamnan Zamfara ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP

Yayin da ake rade-radin cewa Bello Matawalle na jihar Zamfara zai sauya-sheka, wasu gwamnonin APC sun kai masa ziyara a Gusau.

Daily Trust ta bayyana cewa shugaban kungiyar gwamnonin APC, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu ya jagoranci tawaga zuwa Zamfara.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, duk sun gana da Bello Matawalle.

KU KARANTA: Hadimin Jonathan ya jagoranci zanga-zangar da aka yi wa Buhari

Gwamnonin sun yi wa takwaran na su Allah-ya-kyauta ne bayan gobarar da ta barke a wata kasuwa a jihar Zamfara, har su ka bada gudumuwar N50m.

Da yake jawabi, Mai girma gwamna Bello Matawalle ya yaba wa gwamnonin na APC uku, ya ce sun yi abin da abokan aikinsa na jam’iyyar PDP ba su yi ba.

Bello Matawalle ya yi alkawarin cewa zai maida irin wannan alheri da gwamnonin APC su ka yi masa, alamun dai cewa Matawalle ya karbi gwamnonin.

“Wannan dabara ce daga wurin APC, kuma Zamfara a matsayinta na jihar da ba ta kowa ba, za ta cigaba da yi maku maraba.” Inji Gwamnan na Zamfara.

Sauya-sheka: Manyan Jiga-jigan Gwamnonin APC sun ziyarci Gwamnan jihar Zamfara
Gwamnonin APC a Zamfara Hoto:www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugban PGF ya ja-kunnen Shugabannin APC a kan cigaba da zama a ofis

“Ba za mu damu da munanan abubuwan da wasu mutane za su fada ba, mu na kuma sa rai ku aika wa shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari, da gaisuwarmu.”

Majiyar jaridar ta tabbata da cewa ba gudumuwa ta kawo gwamnonin Gusau ba, sun zo ne da nufin kammala shirye-shiyen janye Matawalle zuwa jam’iyyar APC.

Kwanakin baya kun ji cewa Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya na shirin komawa jam'iyyar APC gabannin zaben 2023 domin ya samu ya rike kujerarsa.

Matawalle ya zama gwamnan Zamfara a karkashin jam'iyyar PDP ne bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke a kan rikicin da ya biyo bayan zaben fitar da gwani na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel